BBC Hausa of Friday, 12 February 2021

Source: BBC

Femi Fani-Kayode: Wane ne dan siyasar da ke yawan janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya?

Wane ne dan siyasar Wane ne dan siyasar

Ganawar da fitaccen mai sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Fani-Kayode ya yi da shugaban riko na jam'iyyar APC kuma gwamnan Yobe, Maimala Buni da takwaransa na Kogi Yahaya Bello, ta jawo ce-ce-ku-ce game da alkiblar siyasar Fani-Kayode.

Bayan ganawar tasu, Mr Fani-Kayode, wanda dan jam'iyyar PDP ne, ya ce sun tattauna kan batutuwa da dama wadanda suka shafi siyasa da wasu harkokin ci gaban kasa, lamarin da ya sa wasu 'yan Najeriya suke sukarsa da cewa ko dai yana son sauya sheka ne.

Mutane suna caccakarsa ne ganin cewa ya dade yana ganin baiken gwamnatin da suke ciki, wadda a kodayaushe yake bayyana ta a matsayin wacce ba ta tsinanawa 'yan Najeriya komai ba.

Femi Fani-Kayode, dan kabilar Yarbawa ne daga kudu maso yammacin Najeriya kuma tsohon ministan sufurin jiragen saman kasar, wanda ya yi kaurin suna wajen tayar da kura a shafukan sada zumunta musamman a Twitter da kafafen yada labarai.

Kuma ba wai ya tsaya kawai wajen caccakar gwamnatin APC da shugaba Buhari kadai ba ne, Fani-Kayode mutum ne mai yawan yin kakkausar suka ga duk abin da ya shafi arewacin Najeriya da Hausawa har ma da Musulmai.

Tun lokacin da aka kaddamar da shari'ar Musulunci a wasu jihohin arewacin Najeriya, Fani-Kayode ya ci gaba da sukar lamirin gwamnatocin jihohin da suka kaddamar da ita, da hakan ya sa ya rasa tagomashi a idanun al'ummar yankin arewacin kasar.

Ce-ce-ku-ce

A cikin watan Agustan shekarar 2020 ma sai da Fani-Kayode ya tayar da kura a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta, bayan da aka rika yada wani faifen bidiyo da ya mamaye kafofin inda yake cin zarafin wani ɗan jaridar Daily Trust a Najeriya Eyo Charles.

Dan jaridar dai ya yi masa wata tambaya da ya yi masa da ba ta yi masa dadi ba, a lokacin wata hira da 'yan jarida a birnin Calaba na Jihar Cross Rivers da ke Kudancin Najeriyar.

Har ila yau sarautar "Sadaukin Shinkafi" da Masarautar Shinkafi ta bai wa Fani-Kayode a watan Yulin shekarar da ta gabata ta jawo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen masarautar, inda har wasu masu rike da mukaman sarautar gargajiya suka ajiye mukaman nasu, don nuna adawa da nadin nasa.

    Femi Fani-Kayode: Me ya sa sarautar da aka ba shi a Zamfara ta tayar da ƙura? Halima Yusuf: 'Yar kasuwa na matuƙar kwantar min da hankali - Femi Fani-Kayode Femi Fani Kayode ya tuba bayan ya sha suka daga 'yan Najeriya
Hakan dai ana danganta shi da irin yadda aka san shi da yin suka ga duk wasu al'amura da suka shafi yankin arewacin Najeriyar.

Al'amuran da suka shafi zamantakewa da son mu'amala da mata na daya daga cikin abubuwan da ake danganta Fani-Kayode da shi, inda a watan Satumbar shekarar da ta gabata ya bayyana a shafukan sada zumunta yana musanta rade-radin cewa yana so zai saki matarsa kana ya auri wata tauraruwar wasan Hausa na Kannywood

An dai yi ta yawo da hotunansa shi da Halima Yusuf tana kishingide da shi yayin da suke zaune tare a kan wata doguwar kujerar alfarma.

Amma kuma ya musanta cewa akwai wata dangantaka da ta shafi soyayya ballantana aure, inda ya ce kawarsa ce wacce yake mutuntawa, kuma tana matukar kwantar masa da hankali a kodayaushe.

Rayuwa da kuma karatunsa

An haifi Femi-Fani-Kayode a jihar Lagos, kudu maso yamamcin Najeriya a ranar 16 ga watan Oktobar shekarar 1960 daga kabilar Yarbawa.

Mahaifansa Chief Remilekun Adetokunbo Fani-Kayode da Chief (Mrs) Adia Adunni Fani-Kayode sun rada masa suna David Oluwafemi (ma'ana '' wanda Ubangiji yake so") Adewunmi Fani-Kayode.

Fani-Kayode ya fara karatunsa a Kwalejin Brighton da ke Birtaniya tun yana da shekara 8. Kana a shekarar 1980 ya fara karatu a Jami'ar London inda ya kammala karatun digirinsa na farko a fannin shari'a a shekarar 1983.

kuma shiga Jami'ar Cambridge, inda kakansa, da mahaifinsa da kuma yayansa duka suka yi karatun lauya.

Bayan kammala karatunsa a jami'ar ta Cambridge ne ya dawo gida ya fara karatu a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya inda ya kammala a shekarar 1985.

Ya kuma yanke shawarar tafiya kasar Ghana don yin karatun tauhidi a makarantar koyon addinin Kirista a birnin Accra, inda ya samu takardar difiloma a fannin tauhidin a shekarar 1995.

Ayyuka da mukamansa na siyasa

Femi Fani-Kayode ya taba zama dan jam'iyar (NNC) a shekarar 1989, inda aka zabe shi a matsayin shugaban matasa a cikin wannan shekarar.

Ya kuma samu mukamin babban sakataren yada labarai na shugaban jam'iyar (NRC) na kasa baki daya na farko Chief Tom Ikimi a shekarar 1990, yayin da a shekarar 1990, ya samu mukamin mataimaki na musamman ga tsohon shugaban hukumar tsaron kasa Alhaji Umaru Shinkafi.

A shekarar 1996 ne karkashin gwamnatin mulkin soja ta Janar Sani Abacha, Fani-Kayode ya bar Najeriya inda ya shiga kungiyar (NADECO) a kasar waje inda ya taka muhimmiyar rawa wajen sukar lamirin gwamnatin Abacha.

Amma kuma ya dawo gida Najeriya a shekarar 2001 inda ya hadu da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, lokacin da ya zama mmmba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a shekara ta 2003.

Bayan da shugaba Obasanjo ya samu galaba a zaben ne ya nada Femi Fani-Kayode a matsayin mataimaki na musamman na shugaban kasa kan harkokin da suka shafi jama'a, mukami irinsa na farko da aka taba samu.

Kana a watan Yunin shekarar 2006 ne aka nada shi a matsayin ministan al'adu da Yawon Bude Ido har ya zuwa 7 ga watan Nuwambar shekarar 2006.

Bayan yin wani garanbawul ne a cikin shekarar, aka sauya shi zuwa ma'aikatar harkokin sufurin jiragen sama a matsayin minista har ya zuwa ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007.

A shekarar 2015 aka nada Fani-Kayode a matsayin daraktan yada labarai a karkashin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo.

Fani-Kayode ya sake komawa aikin cin gashin kansa na lauya bayan karewar wa'adin ayyuka da mukamansa na gwamnati.