'Yan bindiga sun saki daliban nan 11 da ma'aikata 3 da aka sace na Jami'ar Greenfield da ke Jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
Kwamishinan tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya tabbatar wa da BBC sakin daliban ranar Asabar.
Yace an babu ko mutum guda da suke zaton ya yi saura a hannun 'yan bindigar, daga bayanan da suke samu ta hannun jami'an tsaro.
"Bayan yara biyar da aka yi wa kisan gilla, ba na jin akwai wani mutum guda da ya yi saura a hannu wadannan bata gari" in ji Aruwan.
Sai dai rahotanni sun ce a gefen titi aka yasar da daliban da kuma ma'aikatan jami'ar da suke tare da su.
Duk da cewa gwamnati da kuma jami'ar ba su bayyana ko an biya kudin fansa ba kafin sakin daliban, amma kafafen yada labarai na cewa sai da iyayen yaran suka biya kudi aka saki yaran nasu.
A ranar 20 ga watan Afrilun da ya gabata ne 'yan bindiga suka shiga cikin ginin da daliban suke kwana inda suka sace su.