BBC Hausa of Saturday, 24 April 2021

Source: BBC

Gwajin farko ya nuna riga-kafin malaria yana matukar aiki

Masana sun yi gwaje-gwajen ne a kasar Burkina Faso Masana sun yi gwaje-gwajen ne a kasar Burkina Faso

Allurar riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro ko maleriya da masana suka kirkiro a Birtaniya, ya nuna nasarar kashi 77 bisa dari na inganci a gwaje-gwajen da aka yi a kasar Burkina Faso.

Masana kimiyya ne suka kirkiro ruwan allurar riga-kafin a Cibiyar Jenner ta Jami'ar Oxford da ke kasar Birtaniya.

Sakamakon ya nuna cewa yana da matukar inganci fiye da ainihin ruwan riga-kafin cutar ta malaria kadai da ake da shi.

An yi gwaje-gwajen ne a kan jarirai da kananan yara masu ta-ta-ta dari hudu da hamsin a kasar Burkina Faso, wanda aka shafe watanni 12 ana gudanarwa.

Yanzu haka za a fara gudanar da gagarumin gwaji kan kananan yara kusan dubu biyar a fadin kasashen Afirka.

Masanan sun ce ruwan riga-kafi ya nuna matukar inganci a gwaje-gwajen, wanda akwai tabbacin yiwuwar rage yawan mutuwar mutane musamman kananan yara da 400,000 da cutar zazzabin cizon sauro ko maleriya ke kashewa a ko wace shekara.

Masana kimiyya a fadin duniya sun jima suna fafutikar ganin sun kirkiri sabbin riga-kafin cutar ta malaria da galibi ta fi addabar nahiyar Afirka.

An jima ana gwaje-gwaje kan nau'in ruwan riga-kafin cutar ta zazzabin cizon sauro "Mosquirix" da kamfanin harhada magunguna na GlaxoSmithKline ya kirkiro, amma kuma ba a samu wata gagarumar nasara wajen kare yaduwar cutar a Afirka cikin shekaru hudu.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ce ta jagoranci shirin a yankunan kasashen Kenya, da Ghana da kuma Malawi.

Sabon ruwan riga-kafin na Oxford shi ne na farko da ya cimma muradan WHO din na ingancin kashi 75 a kan kwayar cutar ta zazzabin cizon sauro.

Zazzabin cizon sauron na kashe mutane fiye da dubu dari hudu a ko wace shekara - akasari kananan yara a Afirka.

Farfesa Adrian Hill, daraktan Cibiyar ta Jenner, inda aka kirkiro ruwan riga-kafin cutar korona ta ce Oxford/AstraZeneca, ya shaida wa jaridar Gaurdia ta Birtaiya cewa yana da yakinin sabon ruwan riga-kafin na zai iya rage yawan mace-macen da ake samu saboda cutar ta zazzabin cizon sauro a kasashen Afirka.

Yaran da aka yi gwaje-gwajen ruwan riga-kafin cutar ta malaria a kan su, da aka wallafa a mujallar Lancet ta Birtaniya, 'yan watanni biyar zuwa sha bakwai ne da ake zaune a yankin Nanoro, yankin da ya kunshi kauyuka 24 da kuma yawan al'umma 65,000 .

Masana kimiyya a Birtaniya sun shafe shekaru suna kasancewa kan gaba-gaba wajen lalubo hanyoyi, da gwaje-gwaje a kan kwayar cutar ta zazzabin cizon sauron.