Agajin gaggawa kan rage girman hatsarin ababen hawa musamman na mota da aka fi samu, a cewar masana.
Yawanci mutane ba su da horo ko ƙwarewa kan yadda ya kamata su bayar da agajin gaggawa lokacin da aka samu hatsari.
Akwai dubaru da matakai da ake bi wajen bayar da agajin gaggawa ga mutanen da suka samu hatsarin mota ko na wani abin hawa.
Masana sun ce mutane da dama ne ke mutuwa sakamakon rashin samun agajin gaggawa a lokacin da suka yi hatsari.
Kuma sanin dubaru da matakan bayar da agajin gaggawa na iya ceto rayuka da dama.
A wasu ƙasashe akwai darasi na musamman kan agajin gaggawa da ake koyarwa a makarantu da wuraren aiki.
Akwai abubuwa uku da ke haddasa hatsari kamar haka:
Ɗabia da halayyar ɗan adam (Human factor)
Matsala daga abin hawa (Mechanical factor)
Matsalar yanayi kamar hanya ko ruwa ko zafi ko hazo (Environmental factor)
Jami'in wayar da kan jama'a na Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Najeriya FRSC Muhammad Kabir Abubakar ya shaida wa BBC cewa an fi samun haɗurra daga ɗabi'a da halayyar ɗan adam.
"Yawanci haɗarurn da ake samu kusan kashi 90 ya fi faruwa ne daga ɗabi'a da halayyar dan adam," in ji jami'in.
Hukumomin sun ce ɗabi'a da halayyar dan adam ta shafi rashin haƙuri da son zuciya da rashin bin dokar tuƙi.
Agajin gaggawa - Matakin farko Idan mutum ya riski hatsari yana kan hanya ko kuma hatsarin ya faru a gaban idonsa, abu na farko shi ne ya fara tunanin kansa a lokacin zai bayar da agajin gaggawa.
Mutum ya tabbatar bai sa kansa ko abin hawansa cikin hatsari ba - ana son ya bayar da tazara tsakanin motarsa ko abin hawansa da inda aka yi hatsarin.
Za a fara nazari kan yanayin hatsarin da muninsa ta hanyar kasa mutune kashi uku da hatsarin ya shafa - Waɗanda suke wayyo Allah wayyo Allah da waɗanda suka fita hayyacinsu ba su san inda suke ba suna halin rai kwakwai mutu kwakwai da kuma waɗanda suka mutu.
Waɗanda suka fita hayyacinsu ya kamata a fara ba agajin gaggawa, kila sun samu toshewar wurin shaƙar iska wato baki da hanci ko kuma zubar jini. Su ya kamata a fara dibawa a ba su agajin da ya dace da zai farfaɗo da su.
Abubuwan da ya kamata a yi
Akwai dubaru da abubuwan da ake yi bayan an gano waɗanda suka fi buƙatar agajin gaggawa domin ceton ransu, kamar waɗanda ba su iya numfashi da masu zubar jini da kariyar wuya ko matsalar lakka.
Ana son a fara kiran lambar kar ta kwana ta hukumar kiyaye haɗurra ta 122 (FRSC emergency number) domin a bayar da cikakken bayanai kan abin da ya faru da kuma inda abin ya faru domin kawo ɗauki cikin gaggawa daga hukumomin da suka fi kusa da wurin da aka yi hatsarin.
Lokacin da aka tunkari wurin motar da ta yi hatsari ana son a fara cire kan batirin motardomin kaucewa duk wani abu da zai haddasa gobara.
Wasu tun a cikin motar ake fara kula da su ta hanyar tayar da wuyansu idan da sarari domin tantance jikinsu domin gano raunin da suka samu.
Sannan a hankali ake cire mutane cikin hikima ba da ƙarfin tsiya ba yadda ba za a haifar masu da wata matsala ba ko munin ciwon kamar matsalar lakka.
Idan an fitar da mutane ana shafa jikinsu a tantance raunin da suka samu tun daga kai har zuwa ƙafa.
A wannan lokacin ake gane waɗanda suke da matsalar lakka, ta hanyar yadda mutane suka tantance su kafin zuwa asibiti.
Matakan farko na agajin gaggawa domin tabbatar da mutum ko yana numfashi ko zubar da jini sosai sun ƙunshi:
Hura iska a baki
Danna ƙirji da tafin hannu (ɗaya saman ɗaya) aƙalla sau 30 ana kuma hura iska a baki
Hana tsiyayar jini ta hanyar ɗaure saman ƙafa ko hannun da ke zubar da jini
Taimakawa kariyar hannu ko ƙafa ta hanyar ɗaure wa da kwali ko tsumma
Waɗanda suka samu rauni sosai ana ɗaukarsu a hankali a ɗora su kan gadon daukar marar lafiya har zuwa asibiti.
Zai fi kyau a ɗauki mutanen da suka yi hatsari a buɗaɗɗiyar mota maimakon rufaffiya don a kwantar da su da kyau.
Taimakon gaggawa yakan taimaka da ceton rayuka tun kafin motar ɗaukar marar lafiya ta iso inda aka yi hatsari.
Hukumar kiyayye haɗuraka ta Najeriya ta ce akwai haɗin guiwa da ta yi da manyan ƙungiyoyin direbobi kamar NURTW da NUPENG da NARTO wajen bayar da horo ga direbobi kan agajin gaggawa idan an samu hatsari da kuma samar da motoci na daukar marasa lafiya.
Jami'in wayar da kan jama'a na Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Najeriya FRSC Muhammad Kabir Abubakar ya kuma ce an tantance wuraren da aka fi samun haɗaruka da yawa a Najeriya.
"An horar da mutanen yankunan kan yadda za su bayar da taimako na gaggawa idan an samu hatsari," in ji shi.
Jami'in ya kuma ce suna ba mutane shawarar tanadi kayan hatsari a mota da suka kunshi bandaji da falasta da abin satsar da jini da sauransu waɗanda ke taimakawa a lokacin da aka samu hatsari ba sai an jira an tafi asibiti ba.