Shugaban makarantar da aka kai wa hari a jihar Neja da ke arewacin Najeriya ya ce ya samu zantawa da maharan da suka sace ɗalibai sama da 100.
Abubakar Alhassan ya shaida wa BBC cewa ya kuma zanta da wasu daga cikin malaman da aka sace tare da ɗaliban.
Maharan sun auka wa makarantar ta Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Tegina ne inda suka yi awon gaba da gomman ɗalibai ƙananan yara waɗanda rahotannin farko suka ce yawansu ya kusa 200.
"Na nemi alfarma kuma na gaisa da maharan inda na nemi a bar daliban cikin koshin lafiyarsu kuma sun yi alkawali amma sun ce ba za su iya fadin yawan daliban ba."
"Malaman da na zanta da su sun ce ba a kashe kowa ba daga cikinsu kuma suna cikin koshin lafiya," in ji shi.
Shugaban Makarantar ya ce duk da maharan sun ƙi bayyana yawan adadin ɗaliban da ke hannunsu amma ya ce bisa bayanan da suka tattara daga iyayen da suka kai wa makarantar rahoton rashin ganin yaransu da kuma ƙididdiga da suka yi sun gano yawan ɗaliban da aka sace.
Ya ce bayan tantance yawan ɗaliban da aka sace, kawo yanzu sun gano ɗalibai kimanin 136 aka tabbatar an ɗauka daga Islamiyyar bayan farmakin da ƴan fashin daji suka kai da yammacin Lahadi.
Ya kuma ce sun tantance cewa malamai guda uku ke hannun ƴan bindigar saɓanin bakwai da ake tunanin tun da farko.
Malamin ya ce daga cikin ɗaliban da aka ɗauka akwai ƴaƴansa guda biyar.
Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba jami'an tsaro umarnin gaggauta ceto ɗaliban Islmiyyar da aka sace a jihar Neja
Ko a watan Fabirairu sai da aka sace ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda 41 a Jihar.
Yanzu satar daliban makaranta a Najeriya ya zama ruwan dare, kuma yanzu satar ɗaliban ta koma har ɗaliban makarantun gaba da sakandare.
A makon da ya gabata ne aka saki ɗaliban Jami'ar Greenfield a jihar Kaduna bayan kashe wasu daga cikinsu. Wannan na zuwa bayan sako ɗaliban Kwalejin gandun daji da ke Kaduna