BBC Hausa of Thursday, 4 March 2021

Source: BBC

Hotunan ban mamaki daga Duniyar Mars

hoto daga Duniyar Mars hoto daga Duniyar Mars

Mutum-mutumin Perseverance na hukumar sararin samaniyar Amurka Nasa ya sauka a Duniyar Mars ranar 18 ga watan Fabrairu da misalin karfe 8:55 na dare agogon GMT, bayan tafiyar wata bakwai da ya shafe yanayi daga duniyar Earth.

Tun daga sannan, ya yi ta aiko hotuna masu kayatarwa daga inda ya sauka a duniyar, wato yankin Ramin Jezero, mai fadin kilomita 49 da zurfin mil 30 daga arewacin tsakiyar Jar Duniyar.

Ga dai wasu zababbun hotuna da mutum-mutumin ke aikowa, a yayin da yake ci gaba da neman wata alama ta ko an taba yin rayuwa a can, da kuma gano yadda yanayin kasa na duniyar yake da yadda sauyin yanayinta yake da kuma kwaso kasar wajen.

An zuba tallafin kudi da zai sa Perseverance ta shafe shekara daya a Mars tana aiki, wanda ya yi daidai da shekara biyu a Earth.