BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

Human Rights Watch: 'Yan bindiga da sojoji sun kashe mutum 310 a Jamhuriyar Nijar a bana

Masu iƙirarin jihadi sun kashe sama da mutum 310 a Jamhuriyar Nijar, inji rahoton HRW Masu iƙirarin jihadi sun kashe sama da mutum 310 a Jamhuriyar Nijar, inji rahoton HRW

Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta ce daga watan Janairun shekarar da muke ciki ta 2021 zuwa wannan watan, masu iƙirarin jihadi sun kashe sama da mutum 310 a Jamhuriyar Nijar.

Lamarin ya sa ƙungiyar yin kira ga sabuwar gwamnatin ƙasar ta Shugaba Mohamed Bazoum ta binciki zarge-zargen laifukan yaƙi da ake zargin sojoji da masu iƙirarin Jihadi sun tafka a ƙasar.

Cikin wata takarda da ta aike wa sabbin ministocin shari'a da na tsaro, Human Rights Watch ta ce akwai buƙatar gwamnati ta gudanar da bincike tare da hukunta waɗanda suke da laifi.

Wasu rahotanni da hukuma ta fitar sun ce da safiyar ranar 15 ga watan Maris, a wani hari mafi muni da aka kai ƙasar, wasu mutane riƙe da makamai sun afka kan ƙauyukan da ke Tillia a jihar Tahoua lamarin da ya kai ga halaka kimanin mutum 137.

Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun bayyana cewa harin ya faru ne a daidai lokacin da mutanen ke ban-ruwa a gonakinsu.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa "yadda ake samun ƙaruwar mace-macen farar hula da wasu da ba a san inda suke ba da kuma daɗuwar hare-haren masu iƙirarin Jihadi, a bayyane take cewa cin zarafin wani ɓangare ya haifar da cin zarafin da sauran ke yi," in ji Jonathan Pedneault, mai nazari kan rikice-rikice a Human Rights Watch.

Human Rights Watch ɗin dai ta nemi sabuwar gwamnatin ƙasar ta yi bincike masu ikirarin Jihadi da sojojin ƙasar kan manyan zarge-zargen cin zarafi 18 da ake yi musu a kan iyakokin Tahoua da Tillaberi tun Oktoban 2019 - Ƙungiyar ta ce ana zargin sojoji da kashe kimanin mutum 185 cikin kisa 496 da aka yi.

Tillaberi da ke iyaka da Mali da Burkina Faso yanki ne da ke fuskantar hare-hare daga masu iƙirarin Jihadi da ke gudanar da ayyukansu a Nijar da ayyukan yaƙi da ta'addanci. Yankin Tahoua da ke iyaka da Mali ma ya fuskanci hare-hare daga mayaƙan.

Ana zargin ƙungiyoyin da ke iƙirarin Jihadi a Nijar da kisan ɗaruruwan jama'a tare da zartar da hukuncin kisa kan masu aikin agaji da shugabannin al'umma da kai hari kan jami'an hukumar zaɓe da hare-hare kan makarantu tun shekarar 2015.

Sannan tun kimanin shekarar 2019, ake zargin jami'an tsaron da ke fafutukar yaƙi da ayyukan masu iƙirarin jihadi da kashe mutane da dama da ake zargi jim kadan bayan tsare su a kasuwanni da kauyuka da kuma janyo ɓatan wasu da dama.

Sai dai babu sahihan bayanai kan wadannan laifuka sannan ba a gudanar da wata tuhuma a kansu ba lamarin da ya ƙara taɓarɓarar da sha'anin tsaron.

Ko a 2020 Human Rights Watch ta tattauna da mutum 12 daga Tillaberi wadanda suka ba da bayanai kan yadda wasu mutane sanye da kayan sojoji cikin motocin jami'an tsaro suka kame tare da cin zarfi har ma da kashe farar hula da mutanen da ake zargi masu ikirarin Jihadi ne.

An sanya wasu daga cikin bayanan mutanen a wani rahoto da wasu masu fafutuka Fulani suka fitar a Mayun 2020.

A jimilla, Human Rights Watch ta samu sunayen mutum 178 da ake zargin an kashe su ba bisa doka ba ko kuma aka tilasta ɓacewarsu da kuma wasu 7 da ake zargin sojojin Nijar sun ci zarafinsu tsakanin Oktoban 2019 da Mayun 2020.

Wani da ya shaida al'amarin da wasu majiyoyi biyu sun ce a ranar 25 ga watan Maris din 2020, wasu mutane sanye da kayan sarki sun isa wani yanki a motocin soji inda kaɓilar Fulani Djalgodji suke zaune fiye da shekara 20 da suka gabata da ke da nisan kilomita 6 daga ƙauyen Adabdabe.

Shaidar ya ce sojojin sun kama Fulani 13 yan shekara 18 zuwa 66 tare da fitar da su daga yankin da kuma kashe su.

A cewar Human Rights Watch, bincike guda ɗaya ta san gwamnati ta gudanar kan zarge-zargen laifuakn yaƙi da ake yi wa sojoji. A Afrilun 2020, tsohon ministan tsaro ya ba da umarnin yin bincike kan zargin ɓatan mutum 102 a Inates da ke yankin Tillaberi a Maris da Aprilun 2020.

Sai dai masu binciken ba su gano wata shaida ba da ke nuna akwai hannun jami'an tsaro, babu wasu bayanai da aka ba da kan dalilin ɓatan mutanen inda aka yi zargin masu iƙirarin jihadi ne da suka yi ba-sa-ja da kayan sojoji ne suka aikata ta'asar.

Wani binciken na daban da Hukumar kare hakkin bil adama ta Nijar ta gudanar daga Mayu zuwa Yulin 2020, an gano wasu kaburbura 6 da aka binne gawarwakin mutun 71 a Inates, wasu kuma aka ba da rahoton sun yi ɓatan dabo sannan aka kammala binciken da cewa ana zargin sojoji ne ke da hannu a al'amarin.

Human Rights Watch na ganin gazawar gwamnatin Nijar ta yi bincike kan wadannan zarge-zargen da sojoji suka aikata kan farar hula na nuna buƙatar lamarin ya koma hannun kotuna da masu bincike.