Inter Milan ta yi nasarar cin Cagliari 1-0 a wasan mako na 30 a gasar Serie A da suka fafata ranar Lahadi.
Tsohon dan wasan Manchester United, Matteo Darmian shi ne ya ci kwallon tilo, saura minti 13 a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon Inter ta yi nasara a wasa 11 a jere a gasar ta Italiya ta kuma ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki 11.
Inter wadda Antonio Conte ke jan ragama na bukatar maki 16 nan gaba daga sauran karawa takwas da ta rage a wasannin Serie A ta bana.
Rabon da Inter Milan ta lashe kofin gasar Italiya tun kakar 2009/10.
AC milan ce ke mataki na biyu a kan teburin Serie A mai maki 63 da tazarar maki daya tsakaninta da Juventus wadda ta doke Genoa a wasan mako na 30 ranar Lahadi.
Juventus wadda take ta uku a teburi da tazarar maki 12 tsakaninta da Inter, ita ce mai rike da kofin Serie A, kuma na tara da ta lashe a jere.