BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Isra'ila ta raunata sama da Falasdinawa 160 a Birnin Kudus

Yawancin wadanda aka ji wa raunin a ka ne da ido da kuma kirji Yawancin wadanda aka ji wa raunin a ka ne da ido da kuma kirji

Sama da Falasdinawa 160 ne aka ji wa rauni a dauki-ba-dadi da 'yan sandan Isra'ila a harabar masallacin Kudus da kuma gundumar Shaikh Jarrah, saboda shirin da hukumomin Israi'la ke yi na tashin Falasdinawa daga muhallansu.

An ga Hotunan bidiyo da ke nuna yadda 'yan sanda ke harba gurneti-gurneti da harsasan roba cikin taron Falasdinawan da su kuma ke jifa da kwalabe da duwatsu

Yawancin wadanda aka ji wa raunin a ka ne da ido da kuma kirji.

Kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta kafa wani asibiti na fili domin yi wa wadanda aka raunata magani saboda asibitocin yankin sun cika makil.

Daman ana zaman tankiya ne tsawon kwanaki inda ake ta dauki-ba-dadi kusan a kullum a kan shirin gwamnatin Isra'ila na korar Falasdinawa daga gidajensu a gundumar Shaik Jarrah da ke yankin gabashin birnin Kudud da Isra'ila ta mamaye. Yahudawa 'yan kama wuri zauna sun karbe unguwar.

Tun kafin yamutsin na yanzu, tun a jiya Juma'a dubban jama'a sun taru a masallacin Kudus domin sallar juma'a ta karshe a watan azumin Ramadan. Da dama daga cikin mutanen sun fantsama tituna domin nuna kin amincewarsu da korar Falasdinawan daga gidajensu.

Hukumomin Isra'ila sun ce an kama masu boren da dama.

Kasashe da sauran wasu hukumomin duniya sun yi rook da a kawo karshen rikicin na Juma'a a kan wannan shiri na korar Falasdiwa.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje ta Amurka ta ce gwamnatin Amurka ta damu matuka a kan yanayin da ake ciki.

Jami'in na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan shirin zaman lafiya a Gabas ta Tor Vennesland, ya bukaci dukkanin bangarorin da ke rikicin da su mutunta ainahin dokar matsayin wuraren masu tsarki na Birnin na Kudus domin tabbatar da zaman lafiya.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da duk wani shiri nata na korar Falasdinawa daga yankin, ta kuma daina amfani da karfin tsiya a kan masu zanga-zanga.

A ranar Litinin Kotun Kolin Isra'ila za ta saurari kara a kan dambarawar da aka dade ana yi kan wannan yanki.

Tun a yakin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967 ne Isra'ila ta mamaye yankin Gabashin Isra'ila, kuma tun daga sannan take daukar birnin gaba daya a matsayin babban birnin kasarta, duk da cewa yawancin kasashe da hukumomin duniya bas u amince da hakan ba.

Falasdinawa na daukar yankin na Gabashin Birnin Kudus a matsayin inda zai kasance babban birnin kasarsu mai 'yanci da suke fata za su samu a nan gaba.