BBC Hausa of Wednesday, 31 March 2021

Source: BBC

Ivory Coast: Laurent Gbagbo zai san makomarsa a Kotun Duniya

Tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo Tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo

A yau Laraba ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, za ta yanke hukunci kan ko ta tabbatar da sakin tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo, shugaban kasa na farko da aka taba gurfanarwa a kotun ta ICC.

Sama da shekara goma da ta gabata ne aka tuhumi Mista Gbagbo da tsohon jagoran matasa na jam'iyyarsa Charles Ble Goude a kotun, dangane da rikicin bayan zabe a kasar ta yankin Afirka ta Yamma.

Sai dai an wanke su kan zargin aikata laifin cin zarafin bil'adama a shekara ta 2019.

Bangaren gabatar da kara ya ja tare da bayyana kin amincewa da hukuncin wanke Mista Lauren Gbagbo, yana mai cewa akwai kura-kurai da aka yi wajen yanke wannan hukunci, inda ya kafe cewa dubban takardu da wasu shedu 96 da aka gabatar yayin shari'ar sun tabbatar da laifinsa ba wata tantama.

Tsohon shugaban na Ivory Coast mai shekara 75, yana zaune ne a Brussels, amma yana fatan komawa gida idan har bangaren mai gabatar da karar ya yi rashin nasara a daukaka karar.

Za a sanya ido sosai a Ivory Coasta, inda tsohon shugaban kasar har yanzu yake da tasiri sosai, a kasar da ke fafutukar samun zaman lafiya na siyasa, kan yadda shari'ar za ta kaya.

Watakila Lauren Gbagbo da tsohon shugaban matasan nasa Charles Blé Goudé su bayyana a zaman sauraren daukaka karar ta hanyar hoton bidiyo, maimakon halartar kotun da kansu saboda matakan dakile cutar korona.

A shekarar da ta gabata an samu mummunan tashin hankali, lokacin da babban abokin hamayyar Mista Gbagbo, Alassane Ouattara ya sanar da aniyarsa ta neman tazarce a wa'adi na uku a kujerar shugabancin kasar ta Ivory coast.

Rikicin bayan zaben na 2010 ya tashi ne lokacin da Laurent Gbagbo, wanda ya kasance a kan mulki tsawon shekara goma, ya ki yarda da shan kaye a hannun Ouattara.