Lokacin da Xueli ta ke jaririya, iyayenta sun bar ta a kasa a wajen gidan marayu. A kasar China wasu na daukar kasancewa zabiya kamar wata la'anta.
Wani yanayi na kwayoyin halitta dake haddasa karancin sinadarin da ke sanya fata launi ya sa fatar jiki da gashinta sun kasance a kode, kana ya sa ba za ta iya jure hasken rana ba.
Amma saboda ta fita daban ya sa Xueli shiga sana'ar tallan kayan kawa.
Yanzu tana da shekara 16, ta mamaye shafukan mujallar tallar kayan kawa na zamani ta Vogue ta kuma jagoranci tallace-tallacen fitattun kamfanonin zayyana tufafi da kayan kawa.
Wannan shi ne labarinta, daga Jennifer Meierhans.
Ma'aikatan gidan marayun ne suka lakaba min suna Xue Li. Xue na nufin dusar kankara a yayin da Li ke nufin kyakkyawa.
An dauke ni riko, kuma a lokacin ina da shekara uku ne ya koma zama da uwar rikona da 'yarta a kasar Netherlands.
Uwar rikona wadda nake kira mahaifiyata ta ce ba za ta iya tuna wani suna mafi kyau ba, daga nan ta yi tunanin yana da muhimmanci ya zama shaidar tushena na kasar China.
Lokacin da aka haife ni a China, gwamnati ta kafa dokar haihuwar da daya kawai a cikin ko wane iyali.
Ka zama marar sa'a muddin ka haifi zabiya.
An jefar da yara kamar ni, wasu an kulle su, ko kuma idan za su je makaranta akan shafa musu bakin shuni a gashin su.
Amma a wasu kasashen a Afirka, ana farautar su, akan yanke gabaobinsu ko a kashe su.
Bokaye da 'yan tsibbu na amfani da kasusuwansu wajen hada magani, saboda mutane sun yi imanin cewa yana warkar da cututtuka, amma ko shakka babu ba gaskiya bane, wadannan camfe-camfe ne.
Na yi sa'a da jefar da ni kawai aka yi.
Iyayena da suka haife ni ba su bar wata alama ba game da ni don haka ban san ranar haihuwa ta ba.
Amma shekara daya da ta wuce, an dauki hoton hannayena don gano sahihiyar shaida kan shekaruna kuma likitoci na tunanin shekara 15 sun yi daidai.
Na shiga sana'ar tallata kayan kawa lokacin ina da shekara 11.
Mahaifiyata ta tuntubi wata mai kamfanin zayyana kayan kawa wacce asalinta 'yar yankin Hong Kong ce.
Tana da ɗa wanda yake da ciwon gaude, sai ta yanke shawarar tana son ta zayyana masa wasu tufafin alfarma don saboda kada mutane su rika kallon bakinsa a koda yaushe.
Ta kuma tambaya ko ina sha'awar shiga shirinta na bikin nuna kayan kawa a Hong Kong.
Na yi matukar jin dadin shiga.
Bayan haka, an gayyace ni zuwa daukar hotuna kuma daya daga cikin su na kamfanin Brock Elbank ne a wurin daukar hotonsa a birnin London.
Ya wallafa hotona a shafin.
Kamfanin masu tallar kayan kawa na 'Zebedee Talent' ya tuntube ni, ya kuma tambaya idan ina son yin aiki da su a shirin su na ganin mutane masu nakasa sun samu wakilci a masana'antar kayan kawa.
An wallafa daya daga cikin hotunan da Brock ya dauke ni a cikin mujallar Vogue ta kasar Italiya na watan Yunin shekarar 2019, wanda aka saka hoton Lana del Rey a shafin farko.
Da farko, ban san irin tagomashin da mujallar ke da it aba, yad au tsawon lokaci kafin in gane dalilan da suka sa mutane ke matukar jin dadin abin ba.
A sana'ar tallan kayan kawa, kasancewa ta daban alkhairi ne ba la'ana ba, kuma ya bude min wata kafa ta wayar da kan jama'a game da kasancewa zabiya.
Tallar kamfanin zayyana kayan kawa na Kurt Geiger wata babbar manuniya ce kan yadda suka ba ni damar nuna bambancina.
Sun amince in yi kwalliya da kuma bayar da umarnin daukar hoton da 'yaruwata saboda dokar korona na nufin mai daukar hoton zai kasance a wani daki daban.
Hakan kuma na nufin zan iya yin abubuwa yadda nake so, kuma ina alfahari da sakamkon.
Akwai masu tallar kayan kawa da suke da tsawon kafa takwas da kuma siranta, amma kuma mutane masu nakasa ko banbanci sun fi fitowa a kafafen yada labarai abu ne mai matukar kyau - amma ya kamata ya zama an saba.
Yawanci akan yi amfani da zabiya wajen tdaukar hotunan don nuna abubuwa kamar fatalwa ko mala'iku, kuma hakan na matukar bata min rai.
Musamman da yake hakan nan una irin wadannan al'adu da tunanin da ke saka rayuwar kananan yara zabiya a kasashe kamar Tanzania da Malawi cikin hadari.
Kasancewa ta zabiya na nufin ina da kashi 10 bisa dari kacal na yanayin gani, kuma ba zan iya kallon haske kai tsaye ba saboda suna raunana idanuna.
A wasu lokuta idan haske ya yi yawa a wurin daukar hoto na kan ce '' Ina iya rufe idanuna ko za ku iya rage hasken fitlar?" ko kuma in ce "Ba damuwa, kuna iya daukar hotuna sau uku da idanuna a bude da hasken fitila shikenan.''
Da farko su kan yi tunanin da akwai wahala amma idan suka dauki hoton farko sai ka ji suna fadin ''Da kyau"' kuma suna matukar farin ciki da sakamakon.
Shugabanni na kan fada wa abokan harkar su '' Idan ba za ku iya shira haka ba, ba za ku samu Xueli ba." Yana da matukar muhimmanci a gare sus u ga cewa hankalina a kwance yake.
Mutane na fada min cewa rashin ganina sosai nan una min wani abu daban ne, kuma na kan ga abubuwa sosai da wasu ba sa iya gani.
Hakan kuma ya sa ba na damuwa da yadda al'ada ko tunanin mutane yake game da kyau.
Me yiwuwa saboda bana iya ganin komai sosai, na kan fi mayar da hankali kan muryoyin mutane da kuma abinda za su fada.
Don haka kyaun su na boye ya fi muhimmanci a wurina.
Ina son tallara kayan kawa saboda ina son haduwa da sabbin mutane, da bitar turancina, da kuma ganin cewa mutane na jin dadin ganin hotuna na.
Ina son yin amfani da tallan kayan kawa wajen yin magana kan zabiya in ce wata matsala ce ta kwayoyin halitta, ba la'anta ba ce.
Yadda za a yi magana a kai shi ne '' mutum mai zabiya' saboda kasancewa ''zabiya'' na nuni nuna kai ko wanene.
Mutane na fada min cewa dole in amince abubuwa na da suka faru a baya amma ina tunanin batun ba haka yake ba.
Na yi amanna kana bukatar ganin abinda ya faru kana ka fahimci dalili ba wai ka amince da da shi ba .
Zan amince cewa ana kashe kananan yara saboda kasancewar su zabiya ne.
Ina son in sauya tunanin duniya.
Ina son sauran kananan yara zabiya - ko wata tawaya daban ko banbanci - su san cewa za su iya yi su kuma zama abinda suke so.
Ni kam, inda da banbanci ta wasu bangarorin amma haka yake ga sauran.
Ina son wasan motsa jiki da hawa sama, kuma zan iya yi sosai haka kowa.
Mutane kan ce ba za ka iya abubuwa ba, amma za ka iya, ka dai gwada.