BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

Jakadan Myanmar a Birtaniya ya ce soja ya kwace masa ofis

An cire jakadan Myanmar a Birtaniya, bayan da ya je ofishinsa da ke London An cire jakadan Myanmar a Birtaniya, bayan da ya je ofishinsa da ke London

An cire jakadan Myanmar a Birtaniya, bayan da ya je ofishinsa da ke London, ya tarar a garkame, kuma jami'in soji da ke ofishin ya hana shi shiga, ya gaya masa cewa yanzu ba shi ne wakilin kasar ba.

Jakada Kyaw Zwar Minn dai ba ya goyon bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Myanmar wata biyu da ya gabata.

An kuma bukaci dukkanin ma'aikatan ofishin da su fita, kana aka kira 'yan sanda don hana su sake shiga ginin.

Zuwan Jakada Kyaw Zwar Minn bakin aiki ke da wuya sai ya tarar kofar ginin ofishin jakadancin garkame, inda jamiin sojin ofishin jakadancin ya hana shi shiga.

Dadin dadawa ma ya gaya masa cewa ai yanzu ba shi ne jakadan ba, duk wani kokari da Chaw Zwar Minn ya yi na burus da wannan magana da neman shiga ofishin abu ya ce tura, sannan, sauran ma'aikatan ofishin daman tuni jamiin sojin sa fitar da su, tare da gayyatar 'yan sanda da su kasa su tsare don hana ma'aikatan sake shiga ofishin.

Jakadan ya bayyana abin da ya faru da juyin mulki a wurin da ya kira gidansa a London; Ya ce , ka duba ka gani , wani juyin mulki ne.

A tsakiyar London, ka dauka irin wannan juyin mulki ne da ba zai taba faruwa ba.'' Kana ganin yadda suka kame min gida. Ni da ne na…. ba gwamnati ba…… Ni da ne na Myanmar''

Jakadan wanda ke rike da wannan mukami tun shekara ta 2014, ya yi hannun riga da sabbin mahukuntar kasarsa Myanmar, sojoji, yana mai suka da kin goyon bayan abin da suka yi a kasarsa na hambarar da gwamnatin farar hula.

Ya bukaci da a kai zuciya nesa kan lamarin kasar tasa, kuma sojojin su saki jagorar mulkin dumokuradiyyar, Aung San Su Kyii, kalaman da suka janyo masa yabo daga Sakataren Harkokin Waje na Birtaniya, Dominic Raab.

Wannan Magana da ya yi da sauran kalamai, ba tare da izinin sabbin shugabannin kasar tasa ba, sun hada shi karo da shugabannin juyin mulkin.

Sojojin sun ce tun wata daya da ya wuce aka yi masa kiranye da ya koma gida, to amma sai a yanzu ne ya gamu da wannan mataki nasu, na hana shi shiga ofishin jakadancin, tun bayan da ya furta kalaman.

Duk da wannan karfin hali da ya yi jakada Kyaw Zwar Minn din ana ganin ko alama bai kai takwaransa, wato jakadan Myanmar din ba a Majalisar Dinkin Duniya, dangane da nuna kin amincewa da juyin mulkin, kasar, inda shi jakadan a majalisar adawar tasa ba ta tsaya ga kin goyon baya ba, har ma ya hada da kira ga kasashen duniya da su murkushe juyin mulkin.

Wannan dai tamkar tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro sabbin hukumomin na Myanmar suka yi, domin aikawa da sako ga sauran jakadun kasar da ke sassan duniya kan su shiga taitayinsu da kame baki, su kuma bi.

Yanzu dai ma'aikatar harkokin waje ta Birtaniya ta ce tana neman sanin matsayin jakadan Myanmar din a London a yanzu, kamar yadda dokokin diflomasiyya suka tana da.