BBC Hausa of Monday, 12 April 2021

Source: BBC

Jihar Imo: Yadda Hausawa ke tserewa saboda fargabar hare-hare

Usman Alkali Baba ne sabon shugaban yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba ne sabon shugaban yan sandan Nijeriya

Baƙi mazauna jihar Imo a Kudu maso gabashin Nijeriya har yanzu na ci gaba da tserewa daga wasu yankuna, sakamakon hare-haren da aka kai musu.

Wasu shaidu sun bayyana wa BBC cewa fargabar da mutanen ke da ita, cewa za a iya sake far musu da kuma rasa abin yi bayan hari da ɓarnar da aka yi musu ce ta tilasta ɗaukar wannan mataki.

A cikin abin da bai fi mako ɗaya ba, 'yan arewacin ƙasar mazauna jihar Imo sun yi zargin cewa an kashe mutanensu aƙalla takwas a wani hari mai kama da na sunƙuru.

Wani dan kasuwa, Alhaji Iliyasu Suleiman ya ce ba fada ba komai ake bude musu wuta inda a cewarsa a yankin Orlu na jihar ta Imo an kashe wasu yara uku bayan bude musu wuta.

"Suka zo Umuaka, suka samu Alhaji Rabi'u suka kashe shi suka kashe yaransa guda uku, shi kuma na baya-bayan nan, yaran Hausawa su hudu ne ƴan Sokoto guda biyu, daya kamar dan Adamawa, dayan kuma dan Nijar ne kawai suka same su suka bude musu wuta". in ji dan kasuwar.

A cewarsa, sun binne gawarwaki da dama - "cikin satin nan mun binne gawa takwas, wadanda suka jikkata akwai mutum shida".

Ya bayyana cewa zuwa yanzu, mutum 60 yan asalin jihar Sokoto da ke zaune a Imo sun koma gida, kuma mutum 24 yan Kano da Katsina suma sun koma jihohinsu na asali.

Alhaji Sani Ahmad Mai rago, wani mazauni a jihar ta Imo ya ce akwai sauran rina a kaba duk da cewa an girke jami'an tsaro a yankin na Hausawa.

"A kashi 100 na Hausawan jihar Imo, wadanda suke zaune a unguwar Hausawa suke kasuwanci ba su wuce kashi 30 ba, nan ne ruhin duk wani bahaushe a jihar Imo". in ji Alhaji Sani Ahmad Mai rago.

Ya ce suna zaune ne cikin zaman dar-dar kuma cikin mawuyacin hali sakamakon fargabar abin da ka je ya zo.