BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Jihar Kaduna : Yadda maƙwabta suka sace yaro dan shekara 5 tare da hallaka shi a Kaduna

Usman Alkali Baba ne sabon shugaban yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba ne sabon shugaban yan sandan Nijeriya

Bayanai na ƙara fitowa fili dangane da kisan wani yaro dan shekaru biyar, da wasu mutum hudu suka yi a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya a wannan mako.

Wani ƙanin mahaifin yaron Sanusi Jibo Magayaƙi, ya shaida wa BBC cewa tun farko an nemi Muhammadu sama ko kasa an rasa a ranar Asabar din da ta wuce, sati guda kenan, kafin daga bisani iyayensa suka samu labarin cewa an gan shi a jihar Kano tare da wani mai suna Galadima.

Ya ce wani dan unguwa ne ya ga Galadima wanda dan unguwar su Muhammadun ne a tashar mota a Kano, lamarin da ya sa ya dauki hotonsa ya aika wa mahaifinsa, sai dai kafin a tura jami'an tsaro sai aka neme su aka rasa.

''Ana nan ana nan wadanda suka yi garkuwa da shi sai suka bugo waya, cewa lallai yaro na hannunsu kuma sai an basu kudi za su sake shi, inda suka nemi Naira miiyan 50, kafin daga bisani aka yi ta gangarowa kasa har aka sakko zuwa Naira miliyan 5''

Ya ce an kai musu kudi inda suka nemi a kai, wato kusa da gadar sama ta Kawo da ke garin Kaduna, amma sai daga bisani aka ki basu yaronsu har tsawon kwana guda.

Magayaƙi ya bayyana wa BBC Hausa cewa mutanen sun yanke shawarar kashe Muhammadu ne saboda zai iya fadar cewa su ne suka sace shi, tun da dama ya sansu a matsayin makwabtan gidansu.

A cewarsa ''An kama Galadima a Kaduna, inda kuma ya shaida wa jami'an tsaro cewa Muhammadu yana Kano, lamarin da ya sa aka tafi da shi da rakiyar jami'an tsaro domin gano marigayin.

Ko da aka je Kano sai ya fara yi musu wasa da hankali, sai da aka kai shi wajen kwamishinan yan sandan jihar Kano aka yi masa barazana da hukunci mai tsanani, sai ya fadi cewa su ne suka kashe Muhammadu.

Ya tababtar da gaskiyar rahotannin cewa Galadima wanda shi aka fara kamawa da hannu a wannan al'amari tsohon sojan Najeriya ne, sai dai an kore shi daga aiki a shekarun baya.

A halin da ake ciki dai a cewrasa an kama mutane hudu da ake zargi da hannu a wannan al'amari, da suka hadar da Nazifi, wanda shi ne ya fara daukar Muhammadu ya mika wa Galadima, da kuma wata mata da aka ajiye yaron a gidanta lokacin da aka boye shi a jihar Kano, da kuma Galadima da wani mai suna Umar, wanda shi ne ya rika yin waya da iyayen yaron.