BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Joe Biden: Waɗanne nasarori shugaban Amurka ya samu a cikin kwana 100?

Joe Biden ne Shugaban Amurka Joe Biden ne Shugaban Amurka

A kan sikeli daya, shugaban kasar na mulkin dimokaradiyyar yana aiki mai matukar kyau.

Shi da aminansa a majalisar dokoki sun yi namijin kokari game da kudirin dokar da ta shafi shirin tallafin korona, kuma suna ci gaba a game da gagarumin kudurinsu na biyu - shirin da za a kashe tiriliyoyin daloli na wanda gwamnatin ta fassara shi a matsayin "kayayyakin more rayuwa."

Kuri'un jin ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa Biden yana da goyon bayan akasarin al'ummar Amurka, nesa ba kusa ba a kan tsohon Shugaba Donald Trump a lokacin da yake a kan mulki.

Amurkawa na daukar yadda Biden ke tafiyar da mulkinsa sannu a hankali na samar da wata dama ta ban iska daga irin salon mulkin Donald Trump mai cike da ce-ce-ku-ce babu kakkautawa.


Gwamnatin Biden har yanzu jaririya ce, amma kwanaki 100 sun nuna wata dama ta duba yadda sabuwar gwamnatin ke gudanar da aiki a cikin yanayi mai cike da kalubale.

Ga wasu daga nasorin da ya samu:

Cutar korona

Idan akwai batu ɗaya da za a iya fada game da Biden fiye da duk wani abu cikin kwanaki 100 na mulkinsa, shi ne yadda ya tunkari matsalar annobar korona.

Yawan mace-mace daga cutar korona a Amurka na kai wa 3,000 ne a ko wace rana a lokacin da Biden ya hau karagar mulki.

Yanzu matsakaicin adadi na kwana bakwai na raguwa da 707. Hakan na nuni da tasirin da shirin gwamnatinsa na kaddamar da riga-kafin ya yi.

Biden ya yi alkawarin samar da ruwan riga-kafin miliyan 100 a cikin kwanaki 100 na mulkinsa.

A yanzu haka Amurka ta zarta miliyan 200, da kusan kasha 52 bisa dari na yawan al'ummar Amurka suka samu aka yi musu akalla riga-kafin sau daya.




Tattalin arziki

Muddin fuskantar bangarorin kiwon lafiyar da suka shafi annobar korona shi ne babban kalubale na farko da gwamnatin Biden ke fuskanta, shawo kan matsalolin tattalin arziki zai kasance na biyu.

Yayin da ake ci gaba da gudanar da allurar riga-kafin kana ana samun raguwar yaduwar cutar korona, binciken jin ra'ayoyin jama'a na nuna cewa Amurkawa sun fi mayar da batun tattalin arziki a kan gaba.

Biden ya karbi ragamar mulki a yayin da kasar ke kan farfadowa daga mummunan tasirin kullen korona na shekarar 2020 ya haifar wa tattalin arzikin kasar.

An yanzu dai, matsalar rashin aikin yi ta ragu, an sake komawa harkokin kasuwanci, kana kasuwannin hannayen jari sun kara tashi sama. Wannan wani labari ne mai dadin ji ga shugaban kasar.

Harkokin shige da fice

Idan har barazanar da annobar korona ke yi kan harkokin kiwon lafiya da tattalin arziki su ne tabbatattun kalubalen mulkin kwanaki 100 na farko na Biden - harkokin shige-da -fice ne suka kasance matsaloli da suka bayar da mamaki.

Shi ne daya daga cikin abubuwan da 'yan tawagar Biden ba su shirya sosai a kai ba.

Saboda damuwa game da kai komon korona a shekarar 2020, wani tunani a tsakanin 'yan ciranin yankin Amurka ta Tsakiya cewa gwamnatin Biden za ta fi zama sassauci, kana sabuwar manufar karbar akasarin kananan yaran da ba sa tare da kowa da suka ketara kan iyakar Amurka da Mexico, adadin 'yan ciranin da ba a tantance ba da ke yunkurin ketera wa Amurkar daga kasar Mexico ya karu matuka.

Kayan aiki na kan iyakar Amurka, wadanda gwamnatin Biden ta ce an yi watsi da su lokacin mulkin Trump sun yi matukar yawa.

Haka kuma, Biden na fuskantar suka daga wasu 'yan siyasa a kan rashin amincewa da daukar mataki kan batun sake tsugunar da 'yan gudun hijira daga adadin 15,000 zuwa 125,000.

Bayan da a baya ya ce a zamanin Trump adadin ya cigaba da kasancewa yadda yake a cikin tsawon sauran shekarun, Fadar White House ta yi sauri ta sauya taku ta ce za a sanar da wani sabo adadi a cikin watan Mayu.

Muddin karuwar 'yan cirani bata yi sauki ba - kana ya shafi mazauna yankin kan iyakoki tare da mamaye kafafen yada labari - matsaloli da kalubalen siyasa za su yi wa Biden yawa.




Alkinta muhalli

Lokacin yakin neman zabensa na shugaban kasa, Biden ya samu wani sauyi mai kyau daga mai matsakaicin ra'ayi game da dokokin kare muhalli zuwa gam ai fitowa kararra ya yi magana kan matsalar sauyin yanayi.

A matsayinsa na shugaban kasa, Biden ya ci gaba da yunkuri kan yin garanbawul ga manufofin harkokin muhalli.

Ya yi sauri ya shiga cikin yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi ''Paris Climate Accord'', ya soke gina bututun mai na matatar mai ta Keystone XL, in da ya fara aikin sake dawo da dokokin da aka janye a lokacin mulkin Trump.

A makon jiya ne ya yi alwashin rage yawan fitar da iskar gurbatacciyar carbon ta Amurka da kashi 50 bisa dari kasa da na shekarar 2005 nan da shekarar 2030.




Manufofi kan kasashen waje

Biden ya fara shugabancin kasar da yin alkawarin kaucewa daga manufofin Trump na "Amurka tukuna", wanda ya rika kauce wa abokantar kasashen waje saboda wani salon mulki na "kai kadai gayya".

Daya daga cikin manufofinsa na kasashen waje da za a lura da shi a ciki kwanaki 100 na farko a mulkinsa shi ne na janyewar Amurka daga kasar Afghanistan wanda aka fara a lokacin shugabancin Trump.

Biden ya kuma kasance mai tafiyar hawainiya wajen batun tattaunawa a teburin shawara ta kasar Iran, bayan da Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliya a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

Ya dauki matakai masu tsauri kan kasar Rasha fiye da wanda y agada, tare da kara aza sabbin takunkumi da ka iya zafafa idan aka kara tsaurarawa.

Jami'an ofishin huddar jakadancinsa sun yi yakin cacar baka da tawagar kasar China kan taka hakkin biladama.


Biden ya kuma kasance mai tafiyar hawainiya wajen batun tattaunawa a teburin shawara ta kasar Iran, bayan da Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliya a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

Ya dauki matakai masu tsauri kan kasar Rasha fiye da wanda y agada, tare da kara aza sabbin takunkumi da ka iya zafafa idan aka kara tsaurarawa.

Jami'an ofishin huddar jakadancinsa sun yi yakin cacar baka da tawagar kasar China kan taka hakkin biladama.

Cinikayya

A shekaru da dama kafin Trumo ya ci zaben shugaban kasa, abubuwa ne da aka amince da su a tsakanin duka bangarorin biyu cewa 'yancin cinikayya wani gagarumin abin cigaba ne ga Amurka da kuma yarjejeniyar kasashen duniya da dama da zai bunkasa kasuwanci da ciniki.

Tsohon shugaban kasar George HW Bush ya kafa cibiyar cinikayya ta Nafta, yayin da sh kuma tsohon shugaba Bill Clinton ya taimaka wajen kafa cibiyar Hukumar Cinikayya ta Duniya.

Bush ya fadada batun 'yancin cinikayya zuwa Tsakiya da Kudancin Amurka. Sannan tsohon shugaba Barack Obama ya nemi tattaunawar yarjejeniyar Gamayyar Cinikayyar Yankin Pacific.

Sai dai kuma tsohon shugaba Trump ya sake daidaita su, wajen amfani da batun biyan kudin haraji mai yawa hadi da barazana kan mayar da martani kan kasuwancin da zai yi daidai da muradun bunkasar tattalin arzikin Amurka.

Mai yiwuwa, za a iya cewa Biden gogagagen dan siyasar kuma mai kare muradan tsohuwar dokar kasa da kasa - ya yi kadan ne a cikin kwanaki 100 na farko a mulkinsa wajen warware abubuwan Trump ya sauya.