Mutumin da ya fi daɗewa a gidan yari a Amurka ya samu 'yanci a baya-bayan nan. Joe Ligon ya tattauna da BBC kan kusan shekara 70 da ya kwashe a jarun, me yasa ya yi wannan dogon zaman, ya ya yake shirin yaruwa idan ya fito.
"Ban taɓa zama ni kaɗai ba. Na fi son in riƙa zama ni kaɗai. Zaman da na yi a gidan yari ya sa na saba da zaman kaɗaitaka, tun daga lokacin da aka tsare ni har lokacin da aka sake ni.
"Hakan na taimaka wa mutane irinmu da ke son zaman kaɗaitaka - ina iya shiga ɗakina na rufe kaina, ban damu da duk abin da ake yi ba. Amma lokacin da aka ba mu damar fara amfani da rediyo da talabijin sai suka koma abokaina."
Za a iya cewa zaman gidan yari duk da ba dadi amma ya yi wa Ligon dadi. Hakan ya taimaka masa wajen yin tunani ta hanyar rufe bakinsa domin gujewa fitina.
Lokacin da aka zo gaɓar da zai bar gidan yarin, abin bai ɗaɗa shi da ƙasa ba, saboda baya da kowa a wajen. A zahiri, neman aboki ba ya cikin zaɓinsa.
"Ba ni da wani aboki a cikin gidan yarin. Ba kuma ni da kowa a waje. Sai dai mafi yawan mutanen da nake da mu'amala da su a cikin gidan, ina daukar su a matsayin abokai. ba mu da matsala da juna," in ji shi.
"Amma ba na ɗaukar haka a matsayin aboki, na fuskanci kiran mutum aboki a wuri na, na da matukar mahimmanci. Kuma da yawan mutane na cewa yin aboki zai iya zama babban kuskure."
Ligon ya bar abubuwa da yawa a baya da ba ya da su. Ya tashi da a hannun kakansa na wajen uwa ne a birnin Birmingham, ba shi da wasu abokai sosai kuma baya zama da iyalan gidansu sosai, yawancin ranar Lahadin yana yini ne yana kallon wa'azi tare da kakansa.
Yana da shekara 13 suka koma kudancin Philadelphia da zama, tare da mahaifiyarsa da ke aikin jinya a asibiti, da mahaifinsa da ke gyaran abubuwan hawa da ɗan uwansa da ƙanwarsa.
Ya yi ta faɗi tashi a makaranta baya iya karatu da karatu. Ba ya iya wasanni.
"Ban fiye fita yawo ba. Ni irin mutanen nan ne masu aboki daya ko biyu kacal, ban fiye son hayaniya ba."
Yayin da Ligon ya fada cikin matsala a yammacin wata Juma'a a 1953, bai san mutanen da yake tare da su ba. Wasu mutane ya hadu da su maƙwabta wadanda suka shaƙu.
"Mun fara tambayar mutane kudi sai muka fara shan barasa da wasu abubuwan na daban..."
Shaye-shayen da suke yi, ya kai su ga yin rikici a wani dare suka yi rikici har ya kai da caka wa wasu wuƙa, mutum biyu sun mutu shida sun jikkata.
Ligon aka fara kamawa a lokacin. A ofishin 'yan sanda ya ce shi ba zai iya tuna tare da su wa ya yi yawo ba a daren.
"Biyun ma da na sani ban san sunayensu na gaskiya ba."
An kai Ligon wani ofishin 'yan sanda da ke nesa da Rodman inda suke zaune sama da kwana biyar, ba tare da samun wani tallafin shari'a ba. Ya ce ya dade yana fushi saboda ko yaushe iyayensa suka zo duba shi sai a kore su.
A wancan lokacin, a lokacin yana shekara 15 kuma ana tuhumarsa da kisan kai - zargin da yake yawan musantawa har lokacin da ya amince ya yi mana wannan tattaunawa, ya ƙi amince da cakawa mutane biyun wuƙa, ya ce wannan jita-jita ce.
"Kai tsaye 'yan sanda suka ba mu takardu muna sanya hannu akai, na sa hannun kan takardar da ta tabbatar da ni na yi kisan kai. Kuma ni ban kashe kowa ba."
Gidan yarin Pennsylvania daya ne daga cikin guda shida da rayuwa ta kai mutumin da ya ce ba ya da laifi. Ligon ya ta fuskantar shari'a kan tuhume-tuhumen, alkalin ya kama mutumin da laifuka biyu.
"Ban san me zan tambaya ba. Amma na san babu mai amince wa da gaskiya ta," in ji Ligon. "Nasan ya kamata na yi wani abu akai, amma kuma ban san me zan yi ba, dole na in karasa rayuwata a gidan yari.
"Zan iya gaya maka shirmen da na yi lokacin ina yawo - ba na iya rubutu ko karatu, ba zan iya rbuta sunana ba. Kawai dai nasan sunana Joe, saboda haka na zaɓi in zama a lokacin idan na tuna kuma ciwo yake mani."
Ligon ya ce maimakon shiga gidan yarin a tsorace sai ya shiga a rude. Babban abin da ke ransa shi ne iyayensa da yan uwansa - "Kan yadda na yi nesa da su da kuma yadda aka kulle ni".
"Wannan wani abu ne da ya kamata ka yi tinani a kai," ya ƙara da cewa.
"Na yi shirme wajen amfani da ƙwayoyi, ba na shan komi a jarun, ban yi komi ba da ya yi sanadin rasa rayiukan mutane. Ban kuma yi kokarin guduwa ba. Ba wanda na lalata wa rayuwa," ya kara da cewa.
"Na zauna a matsayin mutumin kirki a iya ƙoƙarina - mai da hankali kan abin da ke gabana na daga cikin abubuwan da na koya a zamana na gidan yari, ko da yaushe so nake da na yi abin da ke daidai in kuma kaucewa matsala."
Bayan kwashe kimanin shekara 53 a zamansa, an shaida wa Ligon cewa lauya na son ganin sa. Ya ce masa babu wata doka da ta amince a yankewa kananan yara da suka aikata laifi hukuncin kisa.
A lokacin jihar Pennsylvania ta na da fursunonin da aka yankewa irin hukuncin su 525, wanda shi ne mafi yawa a Amurka kamar yadda Bridge ya bayyana.
Jihar Philadelphia ta na da 325 - kuma Ligon shi ne mafi dadewa a cikinsu. Mataimakin mai kare wanda ake kara ya shirya ganawa da shi.
"Ba shi da masaniya kan hukuncin d aka yanke ma sa," inji Bridge. "Bai san komai akai ba, har sai da muka. Abin ban sha'awa ne yadda bai karaya ba, ya nutsu tun daga farko har karshe, a ko da yaushe ya na fatan wani abu zai faru.
"Ba ni da masaniya kana bin da ya ke tunanin zai faru. Ba na jin wannan na daga cikin abubuwan da yak e tunani, kasan wani abun ka iya janyo masa bacin rai, amma sam bai taɓa karaya ba.
Yana da matuƙar haƙuri, yana ganin komai zai daidaita don haka yak e zaune ya na jiran tsammani."
Ganawar ga Ligon, tamkar bude ido ce. A lokacin da Bridge ya nuna masa kwafin takardar da ta kalubalanci daukaka karar kan hukuncin da aka yanke masa, wannan ne lokacin da Ligon ya san ashe an take ƙa'idojin yadda ake tsare da shi.
"A lokacin na gane ba a kyauta min ba tun daga lokacin da aka kama ni. An takura min, na kuma fahimci an yanke min hukunci ba bisa ƙa'ida ba, ta hanyar yanke min hukuncin da babu afuwa."
Shekara 68 ta kare cikin tashin hankali. Yasan ya jira godon lokaci gabanin a sake shi - lokacin da ya kamata kwashe tare da iyalansa, wadanda tuni wasunsu suka mutu.
A yanzu dan shekara 83 ɗin ya samu abin da yake jira na tsawon lokaci, yana da dan shirinsa da yake fatan cimmawa, zai mayar da hankali kan abin da yake ganin shi ne daidai.
"Yar 'yar uwata Valerie ta haihu lokacin ina gidan yari, yayarta ma ta haihu duk ina gidan yarin, ƴarta ma kuma ta haihu," Amma duka yan uwana na kusa sun mutu, mutanen da suka yi saura kawai daga ni sai mahaifiyar Valerie."
"Zan ci gaba da yin abin da na kwashe rayuwata ina yi. A ba ni aikin share-share a matsayin mai lura da abubuwa."