BBC Hausa of Thursday, 15 April 2021

Source: BBC

Johnson & Johnson: Kasashen da suka dakatar da riga-kafin allurar kamfanin saboda matsalar daskarewar jini

Daskarewar jini ya janyo dakatar da yin allurar riga-kafin cutar korona na Johnson & Johnson Daskarewar jini ya janyo dakatar da yin allurar riga-kafin cutar korona na Johnson & Johnson

Kasashen Amurka da Afirka ta Kudu da kungiyar Tarayyar Turai, sun dakatar da yin allurar riga-kafin cutar korona da kamfanin Johnson & Johnson ya samar na wucin gadi, bayan samun rahotannin wasu sun samu matsalar daskarewar jini.

An gano mutum shida da suka samu wannan matsalar cikin kusan miliyan 7 da aka yi wa riga-kafin kamar yadda hukumar ingancin abinci ta Amurka FDA ta bayyana.

An kuma dakatar da yin riga-kafin da aka fara a wannan makon.

Johnson & Johnson ce allurar riga-kafi ta biyu da aka fuskanci matsalar daskarewar jini, baya ga ta AstraZeneca .

Hukumar FDA ta bukaci a dakatar da yi wa mutne allurar na wucin gadi, domin yin bincike kan lamarin. Sannan an tabbatar da mutuwar mutum guda saboda daskarewar jini, yayin da aka kwantar da wani mutum a asibiti inda yake cikin mawuyacin hali.

Dukkan wadanda suka samu matsalar su shida mata ne da ke tsakanin shekara 18 zuwa 48, sun kuma fara nuna alamun ne kwanaki 13 bayan an yi musu allurar riga-kafin.

Bayan ba da shawarar dakatarwar, dukkan cibiyoyin da ake yin allurar da ke Amurka sun dakatar, har sai an gudanar da cikakken binciken inganci da rashin hadarin ta. Ana kuma sa ran jihohi da cibiyoyi masu zaman kansu za su dakatar da hakan.

Amurka ce a sahun gaba na yawan wadanda suka kamu da cutar, inda sama da mutum miliyan 31 suka kamu, sama da 562,000 suka mutu, kuma shi ne adadin mace-mace mafi yawa a duniya.

Johnson & Johnson dai kamfanin lafiya ne na Amurka, amma sashen hada magunguna na kamfanin reshen kasar Jamus wanda aka fi sani da Janssen ne ya samar da riga-kafin cutar korona.

Ba kamar sauran alluran da aka samar ba, Johnson & Johnson allura daya ce ake yi wa mutum, za kuma a iya ajiye ta a cikin kowanne nau'in firji da muke amfani da shi na yau da kullum. Domin haka ne ake iya daukarsa cikin sauki domin kai wa wurare masu nisa ko wadanda ke fama da sauyin yanayi ko tsananin zafi.

Yayin da wasu kasashe suka yi odar miliyoyin nau'in riga-kafin, kasashe kalilan ne suka amince a fara amfani da shi.

Ranar 27 ga watan Fabrairu ne aka amince a fara amfani da allurar a Amurka, amma an fi amfani da riga-kafin kamfanin Pfizer-BioNTech da Moderna a fadin duniya.

An yi wa kusan Amurkawa miliyan 7 nau'in riga-kafin J&J wanda shi ne kashi 3 cikin 100 na wadanda aka yi wa.

Babban mai ba da shawara kan annobar korona Dakta Anthony Fauci, ya ce ya yi wuri a yi tsokaci kan ko za a samu matsala.

Afirka ta Kudu ce kasa ta farko da ta fara amfani da nau'in riga-kafin, amma ta dakatar da ita, duk da cewa babu wani rahoto da aka samu na matsalar daskarewar jini ga wadanda aka yi wa.

Riga-kafin ya samu karbuwa bayan bincike ya nuna yana da karfi da tasiri kan nau'in cutar korona da ta bulla a Afirka ta Kudu, fiye da sauran nau'o'in riga-kafin.

Kuma tun tsakiyar watan Fabrairu, an yi wa kusan jami'an lafiya 300,000 allurar.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa tana bibiyar lamarin, tare da jiran sakamakon rahoton binciken Amurka da Tarayyar Turai.

Har wa yau, ana gab da fara aika wa kasashen Turai nasu kason riga-kafin, a yayin da kamfanin J&J ya sanar da dakatar da yin allurar a Turai baki daya. Duk da cewa ba a fara yin riga-kafin a kasashen Turai ba, amma kwararru sun ce suna jira su ga matakin da Amurka za ta dauka nan gaba.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta soki Tarayyar Turai kan tafiyar hawainiya kan yin allurar riga-kafin, akwai kuma fargabar rashin tsaikon da aka samu a yanzu zai janyo a shiga wani yanayi.

Kawo yanzu ba a fara amfani da riga-kafin kamfanin Johnson & Johnson a Birtaniya ba, duk da cewa ta yi odar guda miliyan 30. Ma'aikatar lafiya ta ce rashin fara amfani da allurar ba zai janyo tsaikon samar da ita a kasar ba, ko kuma koma baya aniyar kasar na yi wa dukkan mutane manya da yara riga-kafin kafin karshen watan Yuli mai zuwa.

Ita ma kasar Canada ta yi odar riga-kafin guda miliyan 10, har yanzu tana jiran a kawo mata na ta kason zuwa karshen watan nan, in ji firaiminista Justin Trudeau.

Ya kara da cewa "Amma duk da haka, muna bibiyar lamarin sau da kafa da jiran sakamakon binciken Amurka."

Me muka sani da daskarewar jini a baya-bayan nan?

Sanarwar hadin gwiwa da hukumar ingancin Abinci FDA da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa CDC suka fitar na cewa: "ana bibiyar rahoton matsalar daskarewar jini ga mutum shida da aka yi wa allurar J&J."

Sanarwar ta ce nau'in daskarewar jinin ya bambanta da wanda aka sani a baya domin haka ana bukatar amfani da wata hanyar ta daban domin magance matsalar.

Sannan maganin da ake amfani da shi ga masu matsalar daskarewar jini mai suna heparin - "ka iya zama hadari idan aka yi amfani da shi ga mutanen".

Kafin a samu karin bayani, hukumar FDA da CDC sun ba da shawarar a dakatar da amfani da riga-kafin nan ta ke har sai an kammala bincike.

Sanarwar hadin gwiwar ta ci gaba da cewa "mutanen da aka yi wa riga-kafin Johnson & Johnson, suka fara jin matsanancin ciwon kai, da ciwon mara, da ciwon kafa, ko daukewar numfashi makwanni uku da yin allurar, su gaggauta tuntubar jami'an lafiya domin ba su taimakon da ya dace".

Sanarwar kamfanin Johnson & Johnson statement

Shi ma kamfanin Johnson & Johnson ya fitar da sanarwa, inda ya ce yana magana da jami'an lafiya da masu ruwa da tsaki kan lamarin.

Sanarwar ta kara da cewa: "Muna sane da abubuwan da suka biyo baya ciki har da masu zub da jni da daskarewarsa bayan an yi musu riga-kafin cutar korona da kamfaninmu ya samar. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan alakar abubuwan da suka faru da riga-kafin da kamfaninmu ya samar."

Damuwa kan ingancin riga-kafin

Daga Rachel Schraer, wakiliyar BBC kan sha'anin lafiya

Kamfanin da ke ba da kariyar lafiya na Amurka, ya gano yar shaidar da ta nuna cewa an samu daskarewar jini ga mutanen da aka yi wa allurar riga-kafin cutar koron ta AstraZeneca.

Gwamnatocin kasashen duniya sun fara alakanta abin da ya faru da sauran nau'o'in allurar riga-kafin, duk da cewa babu shaida kan hakan.

Mutanen da ke wahalar suna da karancin sinadarin da ke taimakawa gyara gurbataccen jini.

Riga-kafin kamfanonin Johnson & Johnson da AstraZeneca na aiki ne kusan iri daya. Domin haka ta wani bangaren ba abin mamaki ba ne idan suka janyo matsala iri guda.

Adadin wadanda suka samu matsalar dan kadan ne, zai kuma yi wuya a gano irin hadarin da daskarewar jinin za ta haifar, amma ga AstraZeneca an yi kiyasin an samu matsala miliyan guda. Yayin da aka samu matsala ga mutum 6 kacal da akai wa riga-kafin Johnson & Johnson cikin kusan mutum miliyan 7.

A takaice, korona na kashe mutum 1 cikin 1000 da ke tsakanin shekara 40 da suka nuna alamun cutar, kuma hadarin na faruwa ga tsofaffi ne.

Da zarar ka fada ajin matasa da shekarunsu suka fada cikin wadanda ba su da tsautsayin kamuwa da cutar korona, za ka tsallake wannan matakin matukar ba ka da wasu nau'o'in cututtukan.