Kungiyar Juventus ta yi rashin nasara a gidan Atalanta a wasan mako na 31 a gasar Serie A da suka kece raini ranar Lahadi.
Juventus ta buga wasan ba kyaftin din tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo wanda ke yin jinya.
Juve ta kasa ratsa bayan Atalanta wadda ta dage sai ta hada maki uku a kan mai rike da kofin na Serie A.
Daga baya Juventus ta koma tsare gida, ko ta tashi da maki daya, idan ba a yi nasara a kanta ba, sai dai saura minti uku a tashi Ruslan Malinovskyi ya zura kwallo a raga.
Da wannan sakamakon Atalanta ta koma ta uku a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Juventus ta hudu mai maki 62, bayan buga wasa 31 a kakar bana.
Wannan kuma shi ne karon farko da Atalanta ta yi nasara a kan Juventus, bayan sama da shekara 20.
A wannan matakin Juventus wadda ta yi harin lashe Serie A na bana na 10 a jere ta kwan da sanin hakan da wuya, bayan da Inter Milan ta daya ta ba ta tazarar maki 12.
Inter Milan za ta fafata da Napoli a karawar mako na 31 ranar Lahadi.
Lazio wadda take ta shida a teburin gasar bana tana da kwantan wasa daya da tazarar maki hudu tsakaninta da Juventus.
Ranar Lahadi, Lazio ta doke Benevento da ci 5-3 kuma wasa na biyar da ta yi nasara a jere a gasar Serie A kenan, ita kuwa Bologna nasara ta yi a kan Spezia da ci 4-1.