BBC Hausa of Wednesday, 2 June 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Gerrard da Benitez da Messi da Sterling da Kane da Lukaku

Steven Gerrard, tsohon kyaftin din Liverpool da Ingila Steven Gerrard, tsohon kyaftin din Liverpool da Ingila

Everton na duba yiwuwar ɗauko kocin Rangers Steven Gerrard ko tsohon manajan Liverpool Rafael Benitez domin maye gurbin Carlo Ancelotti. (Athletic, subscription required)

Ƙungiyar Everton ta kuma sanya sunan tsohon kocin Wolves Nuno Espirito Santo a layin mutanen da take son ɗauko wa. (Talksport)

Tsohon mai tsaron bayan Liverpool Jamie Carragher na da yaƙinin cewa tsohon manajan ƙungiyar Rafa Benitez shi ya fi dacewa da Goodison Park. (Telegraph)

Ɗan wasan Argentine Lionel Messi, mai shekara 33, na gab da cimma sabon kwantiragin shekara biyu da ƙungiyarsa Barcelona. (AS - in Spanish)

Arsenal na kan gaba a cikin ƙungiyoyin da ke son sayen ɗan wasan Manchester Cityna Ingila Raheem Sterling, mai shekara 26, kwangilar da ka iya hana Harry Kane, ɗan shekara 27, koma wa City daga Tottenham. (Sun)

Manchester United na fuskantar babban ƙalubale a fafatawar sayen ɗan wasan Sevilla Jules Kounde yayin da Barcelona ta zaƙu ta dauke matashin ɗan Faransa mai shekara 22. (Mundo Deportivo)

Arsenal ta shirya tsaf domin dauko mai tsaron ragar Cameroon Andre Onana, ɗan shekara 25, da ke taka leda a Ajax, kan £1.7m. (NOS - in Dutch)

Mai ƙungiyar Chelsea Roman Abramovich na fafutikar ganin yadda shi da kansa zai dawo da ɗan wasan Inter Milan asalin Belgium, Romelu Lukaku, kungiyar domin ci gaba da taka leda. (Eurosport)

Za a warewa kocin Chelsea Thomas Tuchel £200m wanda zai kashe a wannan kakar. (Metro)

Ɗan wasan tsakiyar Barcelona dan asalin Bosnian Miralem Pjanic, mai shekara 31, na son komawa Juventus. (Tuttosport)

Sabon kocin Roma Jose Mourinho na shirin dauko mai tsaron ragar AC Milan Gianluigi Donnarumma, ɗan shekara 22. (Mirror)

Yarjejeniyar Leicester City kan ɗan wasan Lille da ke buga tsakiya, Boubakary Soumare, mai shekara 22, za ta kammalu nan bada jimawa ba. (Leicester Mercury)

Brighton na shirya sabuwar yarjejeiya kan ɗan wasan Argentine Alan Velasco bayan Independiente ta yi watsi da bukatar £6m da aka gabatar mata kan ɗan wasan mai shekaru 18. (Football Insider)

Hankalin Manchester United ya koma kan ɗan wasan Sporting Lisbon Pedro Goncalves, mai shekara 22. (Record - via Star)

Leeds United ta shiga yanayi na rashin tabbas bayan takaicin da Stade Brest's ta kunsa mata atayin ɗan wasan tsakiya asalin Faransa, Romain Perraud, mai shekara 23. (Football Insider)