BBC Hausa of Friday, 7 May 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Pellegrini da De Gea da Aguero da Zidane, Benteke da Silva

Dan wasan tsakiya a roma Lorenzo Pellegrini Dan wasan tsakiya a roma Lorenzo Pellegrini

Naɗin Jose Mourinho a matsayin sabon kocin Roma a kaka mai zuwa ya buɗe ƙofa ga ɗan wasan tsakiya Lorenzo Pellegrini koma wa Liverpool, la'akari da cewa sabon kocin zai so ya ɗauko ƴan wasan da ya saba da su, ciki har da mai bugawa Manchester United asalin ƙasar Serbia Nemanja Matic, ɗan shekara 32. (Mirror)

Mourinho na da kuma kyakyawan fata na sake aiki tare da mai tsaron ragar Manchester United da Spain David De Gea, na zaran ya soma horar da Roma. (Todofichajes - in Spanish)

Barcelona ta shiga tattaunawa da wakilan ɗan wasan Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, wanda zai bar Manchester City a wannan kakar.. (Sky Sports)

Arsenal ta yi zarra a cinikin ɗauko ɗan wasan Brighton mai buga tsakiya Yves Bissouma, yayinda suma Tottenham, West Ham da Everton ke kan tuntuɓa. (Express)

Manchester City na da ƙwarin gwiwa a cinikin da take kan ɗan wasa, asalin Mali Bissouma, bayan sakarwa West Ham Declan Rice, mai shekara 22. (Star)

An shaida wa Manchester United cewa za a sayar mata da ɗan wasan Eintracht na Frankfurt mai shekaru 25, Andre Silva, kan £35m a kakar bana.. (Express)

Ba a amincewa Graham Potter, ɗan shekara 45, barin Brighton & Hove Albion domin karban aikin koci a Tottenham ba, in ji shugaban Seagulls, Paul Barber. (Argus)

Kocin Leeds United Marcelo Bielsa na son ɗan wasan baya Ezgjan Alioski, mai shekara 29, ya ci gaba da zama da su. (Yorkshire Evening Post)

Chelsea za ta rabu da wasu ƴan wasanta domin cike gibin kuɗaɗen shigarta a cinikin ƴan wasan wannan kaka, inda ake ganin ɗan wasan Sifaniya Marcos Alonso da Emerson Palmieri, mai shekaru 26, za su bar Stamford Bridge. (Goal)

A ɓangare guda kuma Chelsea da Inter Milan na tababa kan mai bugawa Bosnia tsakiya Miralem Pjanic, wanda Barcelona ke hari tun dawowarsa daga Juventus a kakar bara. (Sport)

Tsohon mai bugawa Ingila, Ashley Young, ya ce yanayi ne ma wahala ya ƙi amincewa da tayin kulob din da ya taka leda tun lokacin da ya ke kan ganiyarsa wato Watford muddin aka nemi shi, kuma bai riga ya sanya hannu a sabuwar yarjejeniya da Inter Milan ba a karshen kaka. (Sky Sports)

Zakaran kofin duniya ɗan Faransa da ke buga gaba Florian Thauvin, mai shekara 28, ya yi watsi da tayin Crystal Palace kuma zai bar Marseille zuwa kungiyar Tigres ta Mexico a wannan kakar. (La Provence - in French)

Ana alakanta Brentford da ɗan wasan Hibernian da Scotland Kevin Nisbet, yayinda kulob din ke shirye-shiryen kaka mai zuwa da yiwuwar sayar da dan wasan gaba Ivan Toney, mai shekaru 25, da ƙungiyoyi irinsu Chelsea da West Ham ke hari. (Sun)

Ƴan wasan Real Madrid na fargabar kocinsu ɗan Faransa Zinedine Zidane, mai shekaru 48, ya "gaji kuma yana cikin takaici" akwai yiwuwar ya bar aiki idan wa'adin kwantiraginsa ya cika. (Goal)

Bayan Madrid ta yi rashin nasara a hannun Chelsea a wasan dab da na karshe na zakarun Turai, ƴan wasa irin su Eden Hazard, da Marcelo da Isco ana ganin suna daf da bankwana da kulob din. (Marca - in Spanish)

Dan wasan Crystal Palace da Belgium Christian Benteke na iya cimma yarjejeniya Fenerbahce, yayinda kwantiragin ɗan wasan mai shekaru 30 ke ƙarewa a ƙarshen watan Yuni. (Sun)

Everton ta miƙa tayin sabon kwantiragi ga ɗan wasan Ingila Joe Anderson yayinda ake samun ƙaruwar kungiyoyin da ke nuna zawarci a kan sa. (Liverpool Echo)

Atletico Madrid ta kwaɗaitu da dan wasan Barcelona mai shekara 21 Riqui Puig. (Fichajes - in Spanish)

Barcelona da Paris Saint-Germain na harin ɗan wasan Monaco mai shekara 23 asalin ƙasar Brazil Caio Henrique. (UOL - in Portuguese)