BBC Hausa of Friday, 19 March 2021

Source: BBC

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Grealish, Ribery, Cavani, Hoppe

Dan kwallon Inter Milan Alessandro Bastoni Dan kwallon Inter Milan Alessandro Bastoni

Liverpool na duba yiwuwar ware £43m domin dauko dan wasan Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 21, wanda Bayern Munich da Barcelona suke zawarci. (Gazzetta dello Sport, via Metro)

Manchester City na kan gaba a yunkurin dauko dan wasan Aston Villa da Ingila Jack Grealish, mai shekara 25, wanda Manchester United ta dade tana son dauka. (Mail)

Kazalika, Manchester City na sha'awar daukar dan wasan Sweden Gabriel Gudmundsson, mai shekara 21, daga kungiyar Groningen ta kasar Netherlands. (Calciomercato.com - in Italian)

Manchester United na duba yiwuwar sayo golan Aston Villa dan kasar Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 28. (Football Insider)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce zai dauki hutun shekara daya idan ya bar kungiyar. (Bild - in German)

Shugaban Boca Juniors Juan Roman Riquelme ya tattauna da dan wasan Manchester United Edinson Cavani, a yayin da kungiyar ta kasar Argentina take fafutukar daukar dan wasan na Uruguay mai shekara 34. (Infobae - in Spanish)

Mai yiwuwa Leicester City da Leeds United su nemi daukar dan wasan tsakiya na Feyenoord Orkun Kokcu, a yayin da ake alakanta Arsenal da Sevilla da yunkurin daukar dan kasar ta Tukiyya mai shekara 20, wanda za a saya a kan £10m. (La Razon, via Leicester Mercury)

Dan wasan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 28, zai jira har sai bayan an kammala gasar Championship ta Turai kafin ya tattauna kan makomarsa a Chelsea, inda kwangilarsa za ta kare a watan Yunin 2022. (Sun)

Liverpool da Tottenham sun bayyana sha'awarsu ta daukar dan wasan Schalke dan kasar Amurka Matthew Hoppe, mai shekara 20. (Transfermarkt, via 90min)

Kocin Derby County Wayne Rooney yana son rike dan wasan Manchester United mai shekara 18 dan kasar Ingila Teden Mengi, a matsayin aro a kakar wasa mai zuwa. (Derby Telegraph)