BBC Hausa of Saturday, 3 April 2021

Source: BBC

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Haaland, Salah, Aguero, Mbappe da Kane

Dan wasan Liverpool da Masar Mohamed Salah Dan wasan Liverpool da Masar Mohamed Salah

Liverpool tana cikin tsaka mai wuya game da dan wasan gaban Masar Mohamed Salah yayin da wasu bayanai a cikin kungiyar suka tabbatar cewa dan wasan mai shekara 28 yana son barin kungiyar. (ESPN)

Manchester United da Chelsea suna son daukar dan wasan Real Madrid dan kasar Sifaniyar Lucas Vazquez, mai shekara 29. (ABC)

Chelsea na son daukar dan wasan gaban Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, idan ya bar Manchester City a bazarar nan idan ta kasa daukar dan wasan gaban Norway Erling Haaland, mai shekara 20, daga Borussia Dortmund. (ESPN)

Real Madrid ta shirya sayar da dan wasan tsakiya Martin Odegaard domin ta samu kudin sayo Haaland. A halin da ake ciki Odegaard yana zaman aro a Arsenal kuma Gunners na son sayen dan wasan mai shekara 22 a mataki na dindindin. (Times)

Sai dai rahotanni sun ce Haaland ya shaida wa Real Madrid cewa yana son murza leda tare da Odegaard a kakar wasa mai zuwa. (Star)

Barcelona tana kallon dan wasan gaba na Inter da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23, a matsayin zabin da ya rage mata idan ba ta dauki Haaland ba. (Sport)

Paris St-Germain za ta duba yiwuwar barin dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya yi gaba a bazarar nan a yayin da ake samun turjiya game da sabunta kwangilarsa. (Le Parisien)

Barcelona za ta kawo karshen zawarcin da take yi wa dan wasan Liverpool dan kasar Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, kuma maimakon hakan za ta bai wa dan wasan da ke tashe dan kasar Sifaniya mai shekara 18 Ilaix Moriba babban matsayi a kakar wasa mai zuwa. (Metro)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya yi amannar cewa dan wasan Ingila Harry Kane, mai shekara 27, yana cike da farin ciki game da halin da yake ciki a kungiyar da ma kasarsa a yayin da ake hasashen zai bar kungiyar a bazara. (Standard)

Inter tana son rike dan wasan Belgium Romelu Lukaku sai dai tayin da aka yi mata na £102m a kansa zai iya tilasta mata sayar da dan wasan mai shekara 27. (Corierre dello Sport)

Leicester City, Crystal Palace, AC Milan da kuma Sevilla suna son daukar dan wasan Marseille da Faransa Florian Thauvin, mai shekara 28, a bazara. (L'Equipe)