BBC Hausa of Thursday, 22 April 2021
Source: BBC
Dan wasan tsakiya na Brazil, Willian, mai shekara 32, ya ce yana da burin ya je ya yi wasa a Amurka, amma kuma sai bayan ya dauki wani kofi da Arsenal tukuna. (Jaridar Goal)
Kociyan Chelsea Thomas Tuchel ya fahimci dalilin da ya sa dan wasan gaba na kungiyar Tammy Abraham, mai shekara 23, ya damu tare da nuna bacin ransa a kan halin da yake ciki a kungiyar.
Wasu rahotanni na danganta tafiyar dan wasan gaban dan Ingila, wanda bai taka wa Chelsea led ba tun ranar 20 ga watan Fabrairu, da tafiya West Ham United. (Jaridar Mail)
Ana kuma rade-radin komawar Abraham din Aston Villa - kungiyar da ya taimaka wa ta samu tsallakawa zuwa gasar Premier League a lokacin da ya je aro a shekara 2019 - Wasu rahotannin ma na cewa Leicester City na sha'awar dan wasan na gaba. (Jaridar Birmingham Mail)
Tottenham Hotspur ta tuntubi kociyan Athletic Bilbao, Marcelino mai shekara 55, dan kasar Sifaniya a kokarin da kungiyar take na maye gurbin Jose Mourinho, wanda ta kora ranar Litinin. (Jaridar Athletic)
Leicester City da Arsenal sun nuna sha'awarsu ta sayen dan wasan tsakiya na tawagar Italiya ta 'yan kasa da shekara 21 Samuele Ricci, mai shekara 19, daga kungiyar Empoli ta Serie B. (Jaridar Tuttomercato)
Kungiyoyin Chelsea da Atletico Madrid da Juventus da kuma Tottenham na sha'awar sayen dan wasan tsakiya, na Palmeiras dan kasar Brazil mai shekara 20 Gabriel Menino. (Jaridar Calciomercato)
Haka suma kungiyoyin Juventus da Roma da AC Milan da kuma Napoli, dukkaninsu na son sayen dan wasan gaba Kaio Jorge, dan kasar Brazil mai shekara 19- daga kungiyar Santos. (Jaridar Calciomercato)
Kungiyar Barcelona ta fara tattaunawa da dan wasan gaba Memphis Depay, dan kasar Holland mai shekara 27, domin daukarsa idan yarjejeniyar zamansa a Lyon ta gasar Faransa ta kare a bazaran nan. (Jaridar Esport3)
Dan wasan tsakiya na Bayern Munich Joshua Kimmich ya yaba da matakin da David Alaba na kungiyarsa ya dauka, na labarin rahotannin da ake yadawa cewa, Alaban zai komaxReal Madrid, da cewa dan wasan bayan dan kasar Austria, mai shekara 28ya yi kyakkyawar shawara. (Jariar Goal)
Zuwan Alaba Real Madrid ka iya tilasta dan bayan Faransa Raphael Varane barin kungiyar, wanda shi kuma aka ce Manchester United na son dan wasan mai shekara 27. (Jaridar Manchester Evening News)
Borussia Dortmund za ta nemi sayen dan wasan gaba na Eintracht Frankfurt da kuma kasar Portugal Andre Silva, mai shekara 25, idan dan gabanta da ake matukar son saye, dan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, ya tafi a bazaran nan. (Jaridar Bild)
Burnley da Newcastle United na ci gaba da nuna sha'awarsu ta sayen dan bayan Benfica Nuno Tavares, mai shekara 21, inda kungiyar ta Primeira Liga ta ce a shirye take a yi cinikin dan bayan na Portugal. (Jaridar Record)
Leeds United za ta koma kan neman wasu 'yan wasan da take hari bayan da aka bayyana mata cewa tsohon dan wasan Ingila na tawagar kasa da shekara 20 Ryan Kent zai ci gaba da zama a Rangers zuwa akalla karin shekara daya. (Jaridar Football Insider)