Manchester City na kokarin ganin ta cimma sabuwar yarjejeniya da 'yan wasan gaba na Ingila Phil Foden, mai shekara 20, da kuma Raheem Sterling, mai shekara 26, kafin karshen kakar da ake ciki, bayan da dan was anta na tsakiya, dan Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 29, ya tsawaita zamansa har zuwa 2025. Eurosport ce ta ruwaito
A wata ruwayar kuma kamar yadda jaridar Telegraph ta ce an dakatar da tattaunawar City din da Sterling - wanda yake da sauran shekara biyu a wa'adinsa na zaman kungiyar har zuwa lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara.
Haka kuma jagorar ta gasar Premier Manchester City ta ce ba za ta ci gaba da zawarcin Lionel Messi ba, mai shekara 33, dan kasar Argentina, har sai ya nuna cewa lalle yana son barin Barcelona. Kamar yadda jaridar Marca ta ruwaito.
Chelsea ta ce a shirye take ta sayi dan wasan gaba na Inter Milan Romelu Lukaku, mai shekara 27 a kan fam miliyan 86.3, idan har ta kasa samun dan wasan gaba na Borussia Dortmun , na kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20. Calciomercato ta Italiya ce ta kawo labarin.
Tottenham za ta yi kokarin sayen dan wasan baya na Southampton dan Denmark Jannik Vestergaard, mai shekara 28, wanda aka kiyasta kudinsa ya kai fam miliyan 18, idan aka bude kasuwar sayen 'yan kwallo, in ji jaridar Express
Liverpool ta gaya wa RB Leipzig cewa ba za ta ci gaba da bukatar sayen dan wasan baya na kungiyar ban a Faransa Ibrahima Konate mai shekara 21 ba Jaridar Bild, ce ta ruwaito daga Express
Kungiyar ta Anfield za ta fuskanci gogayya daga Chelsea wajen neman sayen matashin dan wasan tsakiya na Ajax Ryan Gravenberch, mai shekara 18, dan kasar Holland, wanda ake masa kallon wanda zai maye gurbin Georginio Wijnaldum, shi ma dan Holland, mai shekara 30. Jaridar Gazzetta dello Sport, ta ruwaito daga Express.
West Ham ta ce za ta yi duk abin da za ta iya wajen ganin ta tabbatar dan wasan tsakiya na Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28, wanda ke zaman aro daga Manchester United ya zauna dindindin a kungiyar a bazaran nan. Labari daga Sky Sports
Manchester United ta sanya farashin Lingard wanda ta rene shi tun yana karami a kan fam miliyan 30, kamar yadda jaridar Mirror ta ruwaito.
Ita kuwa kungiyar Arsenal ta sake taso da sha'awarta ta ganin ta sayi dan wasan gaba na Crystal Palace, Wilfried Zaha, 28, dan kasar Ivory Coast, kamar yadda labarin ya fito daga 90min.
Barcelona na son tsawaita zaman dan wasan gaba na Faransa Ousmane Dembele har zuwa shekara ta 2025 kafin bazara. Sai dai kungiyar ta La Liga na da niyyar sanya dan wasan mai shekara 23 a kasuwa, wanda yarjejeniyarsa ta kungiyar za ta kare a 2022, idan ba su cimma matsaya da shi ba. Jaridar Sport ce ta kawo labarin.
Har yanzu Barcelona na sha'awar sayen dan wasan baya na Manchester City, Eric Garcia, amma a wannan karon kungiyar ta rage farashin da ta taya dan wasan dan Sifaniya mai shekara idan aka kwatanta da abin da ta ce za ta saye shi bara, in ji jaridar Marca
Bayern Munich ta tabbatar dan wasan baya na Jamus Jerome Boateng, mai shekara 32, zai bar kungiyar idan yarjejeniyarsa ta kare a bazaran nan. Labari daga Sky Sports ta Goal..
Kociyan Arsenal Mikel Arteta ya bukaci Lucas Torreira ya kwantar da hankalinsa, bayan da aka nemi dan wasan na tsakiya na Uruguay, wanda ke zaman aro a Atletico Madrid ya bar Arsenal ya koma Boca Juniors. Jaridar Mirrror ta ruwaito.
Southampton da West Ham na daga kungiyoyin da ke da sha'awar sayen dana wasan tsakiya na Manchester City Yangel Herrera, shekara 23, wanda a yanzu yake zaman aro a kungiyar Granada ta Sifaniya.Labarin ya fito ne daga Goal