BBC Hausa of Monday, 10 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Salah, Mbappe, Draxler, Borre, Bissouma, Fernandes

Mohamed Salah, dan wasan Liverpool Mohamed Salah, dan wasan Liverpool

Paris St-Germain za ta nemi sayen dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah, dan Masar mai shekara 28, idan Kylian Mbappe dan Faransa mai shekara 22 bai sabunta kwantiragin zamansa ba a kungiyar ta Faransa. (Jaridar Mirror)

Shi kuwa dan wasan tsakiya na PSG din Julian Draxler, dan Jamus mai shekara 27, ya amince ne ya kara zaman shekara daya da kungiyar, yayin da kwantiraginsa zai kare a bazaran nan. (Jaridar Le Parisien)

Kungiyar Watford wadda za ta koma gasar Premier na tattaunawa da dan wasan gaba na Colombia Rafael Borre mai shekara 25, domin komawa can idan kwantiraginsa da kungiyar River Plate ta Argentina yak are a karshen kaka. (Jaridar Sun)

Dan wasan Brighton & Hove Albion Yves Bissouma, mai shekara 24, ya nemi da kungiyar ta bar shi ya tafi a bazara. Manchester City da Liverpool da Arsenal, tare da Marseille, ta Faransa sun nuna sha'awarsu a kan dan wasan tsakiyar na Mali. (Jaridar Times)

Manchester United za ta sabunta kwantiragin dan wasan tsakiya na Portugal Bruno Fernandes bayan wasan karshe na kofin Turai na Europa League, abin da zai sa ta linka albashin dan wasan mai shekara 26 zuwa fam dubu 200 a duk mako (Jaridar Sun)

Kociyan Crystal Palace Roy Hodgson na da kwarin guiwa kungiyar za ta rike dan wasanta na Ingila na tsakiya Eberechi Eze domin kakar 2021-22 duk da yadda dan wasan mai shekara 22 ke bunkasa sosai da sosai. (Jaridar Goal)

Manchester United ta ware fam miliyan 80 domin taya dan wasan gefe na Borussia Dortmund kuma dan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 21. (Jaridar Star)

Dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, mai shekara 21, ya kuduri aniyar ganin yana daga cikin fitattun 'yan wasan da kociyan Chelsea Thomas Tuchel zai rika sanyawa a wasa akai akai, idan ya komo daga aro daga West Brom, abin da ke zaman wani takaici ga Leeds United da Crystal Palace da kuma Newcastle. (Jaridar Sun)

Tottenham ta gaya wa tsohon kociyanta Jose Mourinho kada ya damu kansa da neman sayen dan bayan Ingila Eric Dier, mai shekara 27 da kuma dan wasan tsakiya na Denmark Pierre-Emile Hojbjerg mai shekara 25, idan ya kama sabon aikinsa a Roma a bazara. (Jaridar Sun)

Akwai bukatar hukumar kwallon kafa ta Jamus ta yi saurin daukar kociyan Bayern Munich mai barin aiki Hansi Flick, mai shekara 56, domin maye gurbin Joachim Low a matsayin mai horad da tawagar 'yan wasan kasar, kamar yadda shugaban kungiyar Karl-Heinz Rummenigge ya bayar da shawara. (Tashar Sky Germany )

Mai yuwuwa Lyon ta nemi sayen dan wasan baya na Brazil Renan Lodi mai shekara 23 daga Atletico Madrid. (Jaridar L'Equipe)

Kociyan Bruges Philippe Clement ya ce dan wasansu na gefe dan Holland Noa Lang mai shekara 2, wanda Leeds United, ke so ya gaya wa kungiyar ba zai yanke shawara kan abin da zai yi ba a nan gaba sai kakar wasan yanzu ta kare.(Jaridar GVA)

Leicester City za ta fuskanci gogayya sosai a kan shirinta na zawarcin dan wasan tsakiya na Lille Boubakary Soumare, dan Faransa mai shekara 22, saboda Everton da Wolves da Aston Villa da kuma AC Milan da ta dade tana sonsa na bukatarsa. (Jaridar Foot Mercato)

Stuttgart na tattaunawa da Arsenal a kan sabuwar yarjejeniyar bayar da ron dan bayan kasar Girka Konstantinos Mavropanos, mai shekara 23. (Jaridar Kicker German)

Inter Milan za ta saurari tayi daga kungiyoyi a kan dan wasanta na tsakiya dan kasar Chile Arturo Vidal domin rage yawan kudin da take kashewa wajen biyan albashi. Duk da cewa ana danganta dan wasan da tafiya Marseille, ba wani yunkuri da kungiyar ta yi kan dan wasan mai shekara 33. (Jaridar Calcio Mercato)