BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Sancho, Bale, Hazard, Alli, Lingard, Ramsey

Jadon Sancho, dan Ingila kuma dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho, dan Ingila kuma dan wasan Borussia Dortmund

Borussia Dortmund ta gaya wa dan wasan gaba na gefe dan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 21, cewa zai iya barin kungiyar a bazaran nan. (Jaridar Bild ta Jamus)

Shi kuwa kociyan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer daman ya kafe cewa lalle yana son daukar Sancho a bazara, duk da cewa wasu daga cikin 'yan wasansa suna neman kungiyar ta sayi dan wasan tsakiya na Aston Villa dan Ingila Jack Grealish, mai shekara 25. (Jaridar Telegraph)

Real Madrid ta ce kofarta a bude take domin karbar tayin sayen dan wasanta na gaba na gefe, dan Wales Gareth Bale, mai shekara 31, da kuma dan wasanta na tsakiya, dan Belgium Eden Hazard, mai shekara 30, a bazaran nan. (Sky Sports)

Hazard na son komawa Chelsea ne inda ya baro a 2019. (Jaridar El Chiringuito ta Sifaniya)

Tottenham na shirin sayar da dan wasan tsakiya na Ingila Dele Alli, mai shekara 25. (Jaridar Football Insider)

Luis Suarez ya ce zai ci gaba da zama tare da Zakarun La Liga na bana Atletico Madrid, duk da rahotannin da ake yadawa cewa dan wasan na Uruguay, mai shekara 34 zai koma inda ya fito, Liverpool. (Jaridar Liverpool Echo)

West Ham na fargabar cewa Manchester United za ta hana ta daukar dan wasan Ingila na tsakiya Jesse Lingard, zaman dindindin, bayan da ta aro shi daga United din. Lingard mai shekara 28 ya taka rawar-gani sosai a West Ham a bana. (Jaridar Sun)

Juventus ta ce a shirye take ta sayar da dan wasan tsakiya na Wales Aaron Ramsey, mai shekara 30. (Jaridar Calciomercato ta Italiya)

Barcelona na shirin fara tattaunawa a kan sabuwar yarjejeniya da dan wasan gaba na Faransa Ousmane Dembele.

Kwantiragin dan wasan mai shekara 24 na yanzu zai kare ne a bazarar shekara mai zuwa ta 2022. (Jaridar Mundo Deportivo ta Sifaniya)

Barcelona da Bayern Munich na gogayya wajen neman daukar dan wasan tsakiya na Liverpool da Holland, Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, wanda zai kasance ba shi da sauran kwantiragi da Liverpool. (Sky Sports)

Wolves na tattaunawa da Bruno Lage domin zama sabon kociyan kungiyar. Tun bayan da ya bar Benfica, a bara, Lage ya kasance ba shi da wata kungiya (Jaridar Telegraph)

Kociyan Newcastle Steve Bruce yabayar da tabbacin cewa zai nemi hukumar kungiyar da ta bayar da kudi domin sayen 'yan wasa kafin a bude kasuwar 'yan wasa ta bazaran nan, inda yake son sayen dan wasan tsakiya na Arsenal kuma dan Ingila Joe Willock mai shekara 21. (Jaridar Chronicle)

Newcastle za ta kara bijiro da sha'awarta ta sayen dan wasan tsakiya na Celtic, dan Faransa Olivier Ntcham. Dan wasan mai shekara 25, na zaman aro ne a Marseille. (Jaridar Football Insider)

Mai tsaron ragar Australia Mat Ryan, mai shekara 29, ya nuna cewa mai yuwuwa zai tsawaita zamansa a Arsenal, bayan da yarjejeniyar zaman aronsa daga Brighton ta zo karshe. (Jaridar Mail)

Kwararrun masu shirya fina-finai sun ci gaba da aniyarsu ta yin wani fim a kan kungiyar Leicester da dan wasanta nag aba, dan Ingila Jamie Vardy, mai shekara 34, duk da cewa kungiyar ta kasa samun gurbin kungiyoyi hudu na Premier da za su je gasar Zakarun Turai a rana ta karshe ta gasar bana, karo na biyu a jere.. (Jaridar Mirror)