Kungiyoyin Manchester United da Chelsea da kuma Tottenham na ci gaba da sa ido a kan dan wasan gaba na kungiyar Torino, dan Italiya Andrea Belotti, mai shekara 27. (Jaridar Tuttosport ta Italiyanci)
Watakila Liverpool ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar Rennes, kuma dan Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 18, a lokacin kasuwar 'yan wasa ta bazaran nan da ke tafe, domin maye gurbin Georginio Wijnaldum, dan kasar Holland mai shekara 30, wanda ke shirin barin kungiyar a karshen zamansa a Anfield. (Jaridar Express)
Dan wasan gaba na Borussia Dortmund da kuma Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, shi ne dan wasan da Barcelona ta fi mayar da hankali wajen saye a yanzu. Kungiyar ta Sifaniya za ta so ta saye shi a bazaran nan, amma kuma idan hakan ba ta samu ba to za ta jira har zuwa shekara mai zuwa idan da bukatar hakan. (Jaridar Mundo Deportivo ta Sifaniyanci)
Haka kuma Barcelona ta ce tana da kwarin guiwar cewa cinikin sayen dan wasan baya na Manchester City, kuma dan Sifaniya Eric Garcia, mai shekara 20, zai tabbata nan da zuwa karshen watan Afrilun nan da ake ciki. (Jaridar Sport)
Ita kuwa Juventus tana son sake daukar dan wasan Everton, dan Italiya Moise Kean, wanda ke zaman aro a Paris St-Germain. Sai dai Everton din na son a biya ta fam miliyan 43 da rabi a kan dan wasan gaban mai shekara 21, ko kuma a yi masaya a ba ta dan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 26, ko kuma dan bayan Turkiyya Merih Demiral, mai shekara 23. (Jaridar Gazzetta ta Italiya)
Chelsea na dubu yuwuwar musaya da Juventus, ta bayar da dan bayanta na gefe Emerson Palmieri, mai shekara 26, dan kasar Italiya, ta karbi dan Brazil Alex Sandro mai shekara 30. (Jaridar Calciomercato ta Italiya)
Ita kuwa kungiyar Aston Villa ta gaya wa Chelsea cewa ba ta sha'awar zaman dindindin na dan wasan tsakiya na ingila Ross Barkley, wanda yanzu ke zaman aro a wurinta, to amma kuma West Ham ita ta ce tana sha'awar daukar dan wasan mai shekara 27. (Jaridar TEAMtalk)
Mai horad da 'yan wasan kungiyar Real Betis Manuel Pellegrini yana son daukar dan wasan gaba na gefe na Everton dan kasar Brazil Bernard, mai shekara 28. (Jaridar Fichajes ta Sifaniya)
Sporting Lisbon ta ji dadin aron dan wasan Sifaniya na baya Pedro Porro mai shekara 21 daga Manchester City, saboda haka take son Cityn ta sayar mata da shi ya zama nata dindindin a kan fam miliyan bakwai da dubu 400. (Jaridar Goal)
Newcastle ba ta damu da matsayin kwantiragin Jacob Murphy ba, duk da sha'awar dan wasan gaban dan Ingila da kungiyoyin Watford da Rangers ke yi. Murphy mai shekara 26 zai kasance ba wata yarjejeniya da ke tsakaninsa da wata kungiya a shekara ta 2022 (Jaridar Chronicle)
Tsohon dana wasan baya na gefe na Ingila Ashley Young yana son kare wasansa a kungiyarsa ta farko Watford. A yanzu dai dan wasan mai shekara 35 yana Inter Milan ne. (Jaridar Sun)
Bisa ga dukkan alamu abu ne mai wuya Arsenal ta sabunta zaman dan bayanta na kasar Brazil David Luiz, mai shekara 33, domin kociyan kungiyar Mikel Arteta na sha'awar ci gaba da ba wa William Saliba, dan Faransa mai shekara 20 karin dama a lokacin wasannin gwaji na kafin sabuwar kaka, bayan aron da aka bayar da shi a Nice ya kare. (Jaridar Football.London)