BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Ko Lewandowski zai haura Muller a cin kwallaye a tarihi?

Dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski Dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski

Dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski ya ci kwallo 31 a wasa 24 a kakar 2020/21 a Bundesliga, ya zura 39 a raga a fafatawa 37 a dukkan karawa.

A shekarar 1971/72, Muller ya ci kwallo 40 a gasar Bundesliga a wasa 34 da ya buga, ya ci 50 jumulla a karawa 48 da ya yi wa Bayern a kakar.

Tun daga lokacin aka kasa samun wanda zai tabuka wajen cin kwallaye a gasar ta Jamus ko yin kusa da kwazon da Muller ya yi.

Bayern da Bayern ta samu Lewandowski, wanda ke cin kwallaye da yawa ya sa ake tunanin zai iya maye gurbin Muller.

A kakar bara dan wasan Poland ya kusan tarar da tarihin da Muller ya kafa a Bundesliga, amma ya karkare saura kwallo shida ya yi kan-kan-kan.

A dukkan fafatawa, Lewandowski ya ci kwallo 55 a karawa 47 a 2019/20, kenan ya haura Muller da ya zura kwallo 50 a dukkan wasa 48 kenan, saura cin kwallo 40 a Bundesliga ya rage masa.

Kwazon da Lewandowski ya sa a bara ya kai shi ga zama fitatcen dan kwallon Turai da na duniya da lashe lambar yabo a cin kwallo a Jamus a karo na biyar na uku a jere.

Dan wasan ya taimakawa Bayern Munich ta lashe dukkan kofin cikin gida da na Zakarun Turai da na duniya wato World Club Cup.

Saura wasa 10 a karkare gasar Bundesliga, kuma Lewandowski ya ci kwallo 31 kawo yanzu a wasa 24, inda Bayern Munich ke jan ragamar teburi.