BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Korona: Australia ta hana 'yan kasarta komawa daga India

Gwamnatin Australiya ta haramta wa 'yan kasarta komawa gida daga India Gwamnatin Australiya ta haramta wa 'yan kasarta komawa gida daga India

Gwamnatin Australiya ta haramta wa 'yan kasarta komawa gida daga India, domin kare kasar daga annobar korona da ta yi kamari a Indiyar.

Daga ranar Litinin din nan mai zuwa duk wanda ya karya wannan doka zai iya fuskantar har daurin shekara biyar da kuma tarar kudi.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta Australia, wadda ta sanar da wannan doka da ta ce ta wucin-gadi ce ta ce duk wani dan kasar da ta ya kasance a India a sati biyun da ya gabata to daga Litinin din nan ba shi ba komawa kasar sai a nan gaba.

Duk kuma wanda ya karya wannan doka to an tanadi hukuncin tura shi gidan sarka yai zaman da zai iya kaiwa har na shekara biyar, idan ta kama ma a hada masa har da hukuncin tarar fam dubu 37, sama da Naira miliyan 20.

Nan da ranar 15 ga sabon watan nan na Mayu ne za a sake dubu halin da ake ciki ko dai a sassauta ko kuma a ci gaba da aiwatar da dokar.

Sai dai gwamnatin Australiyar wadda ta ce ta damu da halin da 'yan kasar tata ke ciki a can ta ce ta cimma yarjejeniya da Indiyar don aika mata da kayan agaji da suka hada da na'urar taimaka wa maras lafiya yin numfashi da kuma kayana kariya.

Kasar ta dauki wannan mataki ne, in ji sanarwar bias la'akari da yawan mutanen da aka killace wadanda suka kamu da cutar bayan sun koma gida daga Indiya.

Daman tun kafin sanar w da wannan doka, a farkon makon nan gwamnatin Australiyar ta haramta zuwan dukkanin jiragen sama daga India.

To amma sai wasu 'yan kasar suka bullo da dabarar, tafiya wata kasa ta daban su yada zango kafin daga bisani su tashi zuwa gida, to amma nan ma hukumomin sai suka hana hakan.

Akwai 'yan Australiya akalla dubu tara (9,000) a India, kuma dari shida daga cikinsu na rukunin wadanda ake ganin suna da rauni da za su iya kamuwa da cutar cikin sauki.

Australiya ta dauki matakai daban-daban masu tsauri na hana shigar da cutar daga waje tun lokacin da ta fara a watan Fabrairu na 2020.

Yayin da kasar ke cin amfanin wadannan matakai na dakile cutar ta hanyar rashin samun mutane masu yawa da ke kamuwa.

Kuma mutane 'yan kadan cutar ta kasha idan aka kwatanta da kasashe da dama, tsauraran matakan da gwamnatin ke dauka sun bar 'yan kasar da yawa yashe ba ta yi a kasashen waje.

Wasu 'yan kasar na kokawa da matakin da cewa, kamar a ce iyalai da 'yan uwansu su mutu ne kawai, a Indiya, a ce babu hanyar da za a fitar da su daga kasar, tamkar gwamnati ta yi watsi da su ne.

Kalubalantar wannan doka ta sati biyu da gwamnatin Australiyar ta yi a kotu, abu ne da zai dauki lokaci da kuma tsada.

Koken mutane da mtsin-lamba kawai ake gani za su iya sa gwamtai ta sauya tunani.

Mutanen da ke dauke da cutar korona a Indiya sun karu zuwa miliyan goma sha tara, wadanda suka mutu kuwa sun kai dubu dari biyu jumulla.

A makon da ya wuce a kullum ana samun sabbin kamuwa da cutar dbu dari uku.