BBC Hausa of Thursday, 15 April 2021

Source: BBC

Korona na neman durkusar da asibitocin Brazil

A kiyasi mutane dubu uku ne ke mutuwa kullum a sanadiyyar cutar a Brazil A kiyasi mutane dubu uku ne ke mutuwa kullum a sanadiyyar cutar a Brazil

Jami'an kula da lafiya a jihar Sao Paulo ta Brazil sun ce suna fuskantar karancin allurar rage radadi da ake bukata domin taimaka wa wadanda ke fama da matsalolin rashin lafiya masu tsanani da suka danganci korona.

A kiyasi mutane dubu uku ne ke mutuwa kullum a sanadiyyar cutar a Brazil, wanda hakan ya zarta na ko ina a duniya.

Gwamnan jihar ta Sao Paulo ya aika da sakon gaggawa ga gwamnatin tarayyar kasar da ta aika musu da karin magungunan rage radadi da taimaka wa marassa lafiya, yana mai gargadi da kokawar cewa ayyukan asibitocin gwamnati na dab da durkushewa.

Sao Paulo ita ce jiha mafi yawan jama'a da kuma arziki a kasar ta Brazil. Bayan jihar akwai rahotannin irin wannan matsala daga wasu sassan kasar ma.

Yanayin da ake ciki dai y abaci, domin akwai daruruwan marassa lafiya da ke jiran a sama musu wuri a sassan bayar da kulawar gaggawa a asibitoci, yayin da ake ta karin samun mutane masu kamuwa da cutar ta korona.

Kwararru na dora alhakin hakan a kan sakacin gwamnatin Shugaba Jair Bolsonaro tun da farko, da jinkiri wajen fara allurar rigakafi, da kuma bullar sabon nau'in kwayar cutar wajen haddasa barkewar annobar karo na biyu.

Yanzu dai kasar ta bayar da odar sayen isasshiyar allurer rigakafin da za a yi wa al'ummar kasar baki daya, amma masu sukar gwamnatin sun ce an makaro sosai a wannan yaki,

domin sauran kasashe da ke da karfin arziki na sayen allurer kamar Brazil din suna gaba-gaba a layin jiran rigakafin.

A watan Agusta gwamnatin Brazil ta yi watsi da tayin kamfanin Pfizer na sayen kwalaben allurar rigakafin kamfanin miliyan saba'in.

Sai ga shi kuma a yanzu da abu ya baci ta yi odar kwalabe miliyan dari daya daga kamfanin na Pfizer, amma kuma kusan rabin adadin ba zai samu ba har sai kusan shekarar ta raba.

Cibiyar nazarin harkokin lafiya ta kasar Fiocruz ta ce ta gano nau'in kwayoyin cutar iri daban-daban har casa'in da biyu.

Kuma nau'in da ya fi tayar da hankali shi ne wanda aka yi wa lakabai da P.1, saboda ana ganin yana saurin yaduwa fiye da ainahin nau'in kwayar cutar na ainahi, kuma yana bazuwa a kasashen yankin Latin Amurka da sauran sassan duniya.

Duk da haka masana kimiyya na ganin nau'ukan alluran rigakafin da ake da su a yanzu za su iya aiki a Brazil din, ko da yake ana fargabar ba sosai ba, kuma ma ana tsoron bullar wasu sabbin nau'ukan kwayar cutar ta korona a nan gaba sabanin wadanda aka sani a yanzu.

Dr Nicolelis na cibiyar ya ce; "Brazil ba kawaii ta ce cibiyar annobar koronar ta duniya gaba daya ba, ta ma zama barazana ga kokarin duniya baki daya na yaki da cutar.

Saoda kusan kowa ne mako ana samun wani sabon nau'in cutar a kasar.''