A wani hukunci mai muhimmancin gaske, alƙalai biyar na Babbar Kotun Kenya sun daƙile wani shirin gwamnati da zai sauya kundin tsarin mulkin ƙasar.
Ana yi wa hukuncin kallon mafi girma da muhimmanci tun bayan da aka soke nasarar da Shugaba Uhuru Kenyatta ya yi a zaɓen 2017.
Alƙalan sun ce gyaran tssarin mulkin wanda ake yi wa laƙabi da Building Bridges Initiative (BBI), ba ya kan ƙa'ida kuma ya saɓa wa dokar tsarin mulkin.
Shugaba Kenyatta da takwaransa na hamayya Raila Odinga sun fito da shirin ne bayan an cimma yarjejeniyar zaman lafiya game da zaɓen 2017 mai cike da taƙaddama, wanda kuma ya haddasa rikici a faɗin ƙasar.
Shugabannin sun ce shirin wanda daga cikin sauyin da zai kawo, har da faɗaɗa ɓangaren zartarwa, suna masu cewa zai ƙara mayar da gwamnati ta jama'a sosai.
Sai dai masu suka na cewa yunƙuri ne kawai da zai dinga saka wa 'yan siyasa sannan kuma ya jawo kashe-kashen kuɗaɗe a gwamnati da majalisa, waɗanda ƙasar ba za ta iya ba saboda da ma bashi ya yi mata yawa.
Majalisun wakilai da ta dattawa duk sun amince da shirin wanda ke jiran sa hannun shugaban ƙasa kafin kotun ta soke shi a ranar Alhamis. Ba don haka, da 'yan Kenya sun fita kaɗa ƙuri'ar raba-gardama kafin babban zaɓen ƙasa a shekara mai zuwa.
Me alƙalan suka ce?
Yayin wani jawabi ta talabijin, alƙalan sun ce Shugaba Kenyatta ya karya kundin tsarin mulki saboda ɓullo da shirin da ya kamata a ce 'yan ƙasa ne suka ɓullo da shi.
Kazalika sun ce kwamitin aiwatar da shirin na BBI, wanda shugaban ya ƙirƙira, ba ya kan doka, suna masu cewa Mista Kenyatta ya gaza a shugabancinsa.
Sun yi gargaɗin cewa za a kai ƙarar shugaban a matsayinsa na mutum ba shugaban ƙasa ba.
"Hanyar da aka sani wajen gyaran kundin tsarin mulki ita ce, 'yan ƙasa ne kaɗai za su iya ɓullo da ita ba gwamnati ba," a cewar alƙalan.
Wannan hukunci ka iya samar da dalilin da zai sa a tsoige shugaban ƙasa, sai dai abu ne mai wuya majalisa, wadda ita ce ta amince da shirin tun da farko, ta soma yunƙurin tsige Kenyatta.
Me shirin BBI ya ƙunsa?
Shirin ya nemi a ƙirƙiri muƙamin firaminista da sabbin mazaɓu 70 da kuma wata ayar doka da za ta ba da damar ƙirƙirar sabbin 'yan majalisa kusan 300 waɗanda ba zaɓaɓɓu ba.
Kenyatta da Odinga na cewa sauyin zai sauƙaƙa rikicin siyasa a ƙasar idan aka rage tsarin nan na wanda ya ci zaɓe ya kwashe duka.
Sai dai wasu na cewa kundin tsarin mulkin ƙasar wanda aka ayyana shi a shekarar 2010 an same shi ne ta hanyar haɗin kan al'umar ƙasar kuma ya yi aiki duk da yunƙurin 'yan siyasa na kawo masa naƙasu.
Rikicin siyasa ne ya haddasa kisan mutum fiye da 1,500 kuma ya raba da yawa da muhallansu bayan zaɓen 2008.
Mene ne tasirin hukuncin a siyasance?
Lamarin BBI ya karaɗe lungu da saƙo na siyasar Kenya a cikin shekara biyu da suka wuce, saboda haka hukuncin wani naƙasu ne ga Mista Kenyatta wanda ya so ya aiwatar da sauyin a matsayin babban aikinsa wanda ba za a manta da shi ba.
Haka ma yayin neman amincewar 'yan majalisar, an kai ruwa rana ta yadda har sai da aka yi zargin cewa gwamnati ta bai wa 'yan majalisa cin hancin dala 1,000 kowannensu, kamar yadda wani ɗan majalisa ya shaida wa BBC.
Duk da cewa minsitan shari'a ya ce gwamnati za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun, amma masana shari'a na cewa da wuya a samu wani sauyi a hukuncin.
Mista ya ba ya jituwa da ɓangaren shari'a tun bayan da Kotun Ƙoli ta soke zaɓensa shekara huɗu da suka wuce, abin da ya jawo zuwa zagaye na biyu. A lokacin ya yi gargaɗin cewa zai gyara kotunan.
Ya sha ƙin bin umarnin kotu a 'yan shekarun nan kuma wasu na tunanin wannan karon ma ba zai bi umarnin na ranar Alhamis ba.