BBC Hausa of Wednesday, 28 April 2021

Source: BBC

Kowacce kasa za ta je gasar nahiyar Turai da 'yan wasa 26

A wani sabon shiri, kowacce tawagar kwallo a Euro 2020 za ta je da 'yan wasa 26, maimakon 23 A wani sabon shiri, kowacce tawagar kwallo a Euro 2020 za ta je da 'yan wasa 26, maimakon 23

Kowacce tawagar kwallon kafa da za ta buga gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana, za ta je da 'yan wasa 26, maimakon 23 da aka saba.

An yi wannan sauyin ne don rage gajiya ga 'yan kwallo, bayan da suka buga wa kungiyoyinsu wasanni dab-da-dab, sakamakon bullar cutar korona.

Hakan zai taimakawa masu horar da tamaula samun saukin zabar 'yan kwallo koda annobar ta taba wata tawagar.

An kuma amince kowacce tawaga ta sauya 'yan wasa biyar-biyar a kowacce karawar.

Tun a bara ya kamata a buga gasar cin kofin nahiyar Turai wadda ta ci karo da cutar korona da ta sa aka dage zuwa 11 ga watan Yunin 2021.

An tsayar da ranar 1 ga watan Yuni domin tawagogin su mika sunayen 'yan wasan da za su buga musu gasar.

Ana sa ran cikin makon 24 ga watan Mayu kocin tawagar kwallon kafa ta Ingila, Gareth Southgate zai bayyana 'yan wasansa.