Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Kaduna Sheikh Dr. Tukur Almanar ya ce a baya ya so shiga aikin soja, amma kuma sai ya bi hanyar malanta, kuma yana alfahari da kasancewarsa malami.
Dr. Tukur ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da BBC Hausa a cikin shirin Ku San Malamanku inda ya ce ya gode wa Allah da ya kasance malami, kuma ya bi hanyar da iyayensa suka daura shi a kai.
Yana cikin malaman da suka shahara a Kaduna, inda yake da makarantar da ake karatuttuka daban-daban, kama daga bangaren boko da ta matan aure da maza magidanta da kuma Islamiyya ta yara.
Wane ne Sheikh Tukur Almanar?
Cikakken sunansa shi ne Muhammad Tukur Adam Abdullahi. Ya samu sunan Almanar daga makarantar Almanar da yake jagoranta da ke Unguwar Rimi a tsakiyar birnin Kaduna.
An haife shi ranar 3 ga watan Oktoban 1970 a kauyen Fan Lo da ke Karamar Hukumar Barikin Ladi ta jihar Plateau.
Sheikh Tukur Bafulatani ne cikin ƙabilun Bararoji da ke yin kitso. "Domin har lokacin da nake firamare ina da wannan kitson," in ji Sheikh Tukur.
Ya yi makarantar firamare ta Razek Primay School sannan ya kammala a makarantar Dorawan Babuje, kuma a lokacin ne ya kammala izu 30 na Alkur'ani.
Malamin ya fara makarantar sakandare ta Nakem Memorial School, sai dai daga baya ya sauya layi, inda ya koma makarantar koyon Larabci ta Alin Iliya Memorial School a 'yan taya da ke garin Jos.
Sheikh Tukur ya kasance cikin daliban farko na babbar sikandaren Izala a karkashin Sheikh Isma'ila Idris Zakariyya a Rafin Fa.
An dauke shi malami a makarantar a shekarar da ya kammala.
Bayan ya shafe shekara daya yana koyarwa, ya samu gurbin karatu a jami'ar Musulunci ta Madina a 1990, inda ya yi digiri a fannin shari'ar Musulunci.
Ya yi aiki da wata cibiyar addinin Musulunci mai babban ofishinta a Kano mai suna Al-muntadal Islamiy tsawon shekara shida. Ya kuma yi aiki da cibiyar a Kano da Kaduna.
Ya samu damar tafiya ƙasar Sudan, inda ya yi digiri na biyu da na uku a fannin shari'a a Jami'ar Bakhtu-Rrida.
Su wanene malaman Shiekh Tukur Almanar?
Shiekh Tukur Almanar ya ce yana alfahari da malamai da dama a matakan karatukansa. Malaman sun hadar da Sheikh Abdallahi Idris da Sheikh Abdulaziz Yusuf da Malam Isa Pele.
Daga cikin malaman da suka fi yin tasiri ga Sheikh Tukur akwai Sheikh Ismaila Idris Zakariyya da Khalifansa Sheikh Sani Yahaya Jingir da Hassan Sa'id Jingir da Dr. Alhasan Sa'id da Sheikh Hasan Dikko.
Haka kuma ya ce akwai wasu hamshaƙan malaman da ya tasirantu da su yayin zamansa a Madina.
Tambayoyin da aka fi yi masa
Dr. Tukur Almanar ya ce tambayoyin da aka fi yi masa sun kasu biyu.
Ya ce: "Gaskiya a ɓangaren mata tambayoyin da aka fi yi min su ne a kan abin da ya shafi jini na al'ada da rikice-rikicensa. Wata za ta je ta sha kwayoyi saboda taƙaita haihuwa ko tsarin haihuwa, sai al'adarta ta rikice mata ta birkice mata."
Ya ce a ɓangaren maza kuma an fi yin tambayoyi a kan wasu harkokin kasuwanci, hallaccinsu ko haramcinsu.
Da yake Sheikh Tukur ya taso ne cikin Fulani, ya ce ya yi kiwo da noma sosai a ƙururciyarsa. Ya ce shi kaɗai yana iya kiwon garke guda na shanu, wato shanu 100.
Ko malamin ya yi wasanni a ƙuruciya?
Almanar ya ce ya yi wasanni guda uku; wasan ƙwallon ƙafa, inda ya riƙa buga lamba bakwai, da wasan gudu da kuma wasan kokawar Takwando.
Iyali
Dr. Tukur ya ce yana da mata huɗu da 'ƴa'ƴa 12. Sai dai ya ce har yanzu mata suna aiko masa da bukatar cewa suna son ya aure su, abin da ya bayyana da cewa ba mai yiwuwa ba ne.