BBC Hausa of Monday, 17 May 2021

Source: BBC

Kudancin Najeriya: Matakin gwamnonin yankin na hana kiwo ya janyo muhawara

Gwamnonin jihohi 17 na kudancin Najeriya sun yanke hukumci kan kiwon dabbobi a gari Gwamnonin jihohi 17 na kudancin Najeriya sun yanke hukumci kan kiwon dabbobi a gari

Ana ci gaba da bayyana damuwa game da shawarar da gwamnonin jihohi 17 na kudancin Najeriya suka yanke ta hana kiwon dabbobi a gari, a duk fadin yankin, da kuma hana makiyaya yawo da dabbobinsu.

Wasu makiyaya da abin ya shafa dai sun ce, aiwatar da wannan tsari abu ne mai matukar wuya, kuma zai jefa su cikin halin tsaka mai wuya.

Wani Bafullatani makiyayi a jihar Osun wato Aliyu Salihu, ya ce kiwon da suka gada kaka da kakanni shine na zagayawa da dabbobinsu domin ganin sun samu abinci, don haka wannan mataki da mahukunta a yankin suka dauka na killace su a waje guda ba abu ne da suke da ilimin yi ba, don haka ba abun da zai haifar face cutar da su.

''To ina ma za mu nemo abincin da za mu ba wa dabbobinmu, ?, ko akwai wani tanadi da suka yi mana ne ?, in dai ana son a hana kiwo sai a duba abin da ya kamata a yi nan da shekara 10 ba wai lokaci daya kawai a zo a ce an hana kiwo ba,'' inji shi.

Shima wani bafullatani dake jihar Delta Abdulkarin Usman ya ce su ba wani abu suke nema daga gwamononin yankin ba illa kawai a barsu su gudanar da sana'arsu ta kiwo cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

''Mu bamu ce a bamu wuta ko a bamu ruwa ba, cewa kawai muka yi a baru mu mu yi sana'armu, mu bamu ce a cikinsu babu bata gari a cikinmu ba, amma kamata ya yi a bincike a gano su a dauki mataki a kansu, mu kanmu basu barmu ba'' inji shi.

Abun da masu fashin baki ke cewa

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum kamar Tafida Isah Mafindi wanda shi ne yariman Muri, na ganin cewa gwamnonin yankin basu da ikon daukar wannan mataki.

A cewarsa dokar kasa ce ta bawa kowanne dan Najeriya ikon zama a duk inda ya gaba dama domin gudanar da harkokin shi cikin aminci ba tare da kowanne dan kasa ya shigar masa hanci da kudundune ba.

''Yadda aka yadda Inyamuri ya bude kanti a Abuja, ko Zamfara ko Kaduna, haka za a yi kiwo a Oyo, za a yi kiwo a Enugu, za a yi kiwo a Osun da Benue, wannan tsarin mulkin Najeriya ne ya bawa kowa damar haka,'' inji Mafindi.

Gwamnonin kudancin Najeriyar su 17 dai sun dauki wannan mataki ne da baki daya, duk da banbancin ra'yin siyasa da ma na jam'iyya da ke tsakaninsu.

Wasu daga cikin 'yan majalisar dattawan kasar kamar Sanata Ali Ndume, suma suna ganin cewa gwamnonin basu yi abinda ya dace ba.

An rawaito Sanata Ndume na cewa ''Na yi tunanin gwamnonin nan za su je su gana da shugaban kasa ne domin gabatar da abubuwan da suka tattauna, ko ma su bamu mu a majalisa mu yi aiki da su, amma sai suka ɓige da gabatar da wata sanarsu a gaban 'yan jarida.''