BBC Hausa of Wednesday, 10 March 2021

Source: BBC

Kungiyar kwadago a Najeriya za ta yi zanga zanga

Kungiyar kwadago a Najeriya za ta yi zanga zanga Kungiyar kwadago a Najeriya za ta yi zanga zanga

Rassan ƙungiyoyin da ke jihohin Najeriya sun amsa goron gayyatar uwar kungiyoyin kwadago ta kasar, NLC, kuma har sun yi taro a birnin Abuja domin share hanyar zanga zangar da suka ce ta kasa ce baki daya.

Sun kuma ce za su yi zanga zangar ce domin nuna rashin amincewa da wata doka da majalisun dokokin Najeriyar suke shirin zartarwa, wadda suke zargin za ta bai wa gwamnatocin jihohi zabi wajen biyan albashi mafi kankanta, sabanin naira dubu talatin da gwamnatin tarayya ta amince da shi.

"Mun yi mamakin inda su ke neman cewa a maganar mafi kankantar albashi a bar wa gomnoni a jihohinsu su aiwatarwa da abin da ya shafi karin albashi"" in ji Comrade Kabir Nasir wanda shi ne jami`in tsare-tsaren kungiyar kwadagon.

Sai dai binciken da wakilin BBC ya yi a tsakanin wasu `yan majalisar dokokin Najeriyar ya nuna kudurin da suke shirin zartarwa bai ci karo da muradan `yan kwadagon ba.

`Yan majalisar sun yi ikirari cewa , kudurin yana nema ne ya ga an cike gibin da ake samu tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya ta fuskar biyan albashi mafi kankantar, ta yadda gwamnatin tarayya za ta iya tallafa wa jihohin da suka gaza wajen biyan sabon albashin daga bisani sai a warware a hankali.

Amma `yan kwadagon, ga alama ba su gamsu da wannan hanzarin ba.

A watan Oktoban 2018 ne Uwar kungiyar kwadagon Najeriyar ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya a kan albashi mafi kankanta na naira dubu talatin.

Tun daga wancan lokacin wasu jihohin suka fara biyan ma`aikatansu, yayin da wasu kuma suka daidaita a kan wani adadi, saboda a cewar su ba su da sukunin biya tun da ba su da gashin gwamnatin tarayya.

Suna cikin irin wannan daidaitawar ce aka fada cikin bala`in annobar korona!..

Annobar korona ta nakasa hanyoyin samun kuɗin shiga ga jihohin ƙasar da dama, abin da ya sa mafi yawansu ba sa iya biyan mafi ƙarancin albashin naira dubu talatin cikin sauƙi.