BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Kungiyoyi da 'yan wasa sun yi wa shafukan zumunta yajin aiki

Kungiyoyin kwallon kafa da 'yan wasa na zanga-zangar ne domin cin zarafi da kuma wariya Kungiyoyin kwallon kafa da 'yan wasa na zanga-zangar ne domin cin zarafi da kuma wariya

Kungiyoyin kwallon kafa da 'yan wasa da 'yan guje-guje da tsalle-tsalle sun fara wata zanga-zanga ta kwana hudu kan kafafen sada zumunta domin gujewa cin zarafi da kuma wariya da ake nunawa mambobinsu.

An fara zanga-zangar ne a ranar Juma'a da da misalin karfe 3:00 na rana za kuma a kammala ranar Litinin da karfe 11:00 na dare.

Matakin nuna goyon baya domin kyamar masu cin mutuncin a intanet da fatan kamfanonin su dauki mataki kan nuna wariyar launin fata da kuma zagi da ake yi wa mutane.

Kungiyar kwallon zari zuga da masu kwallon gora sun shiga zanga-zangar.



Hukumomin Premier sun ba da wata sanarwa gabanin wannan mataki da za su dauka na kwanaki hudu, wadda take cewa ba za ta daina kalubalantar kamfanoni ba har sai sun dauki mataki kan masu nuna wariya a kafafen yada labarai a fanni wasanni da sauran fanno ni na rayuwa.

"Mun san cewa dakatar da amfani da kakafen kadai ba zai kawo karshen wannan lamari ba, wanda shi ya sanya muke ci gaba da daukar matakan da za su kawo sauyi,"in ji sanarwar.

Yan wasa da dama sun wallafa sanarwar a shafukansu gabanin fara wannan zanga-zanga, wasu kungiyoyin kuma sun sauya fuskar shafinsu na Twitter zuwa baka kirin.

Dan wasan Mancheter City Raheem Sterling ya wallafa cewa za mu rufe shafukanmu na sa da zumunta daga karfe 3 na yamma a yau zuwa ranar Litinin 3 ga watan Mayu, domin kawo karshen cin mutuncin da ake yi a kafafen sada zumunta.

Dan wasan Leeds United Kalvin Phillips ya rubuta cewa "Abin takaici yau mu ne muke daukar wannan mataki. Kamata ya yi kafafen sada zumunta su zamo wurin nutsuwa ga kowa.