BBC Hausa of Monday, 22 March 2021

Source: BBC

Lafiyar kwakwalwa: An samar da layin waya a kyauta domin taimakon masu fama da matsananciyar damuwa a Najeriya

Wannan aikin na kyauta na gudanane cikin harsunan Hausa da Igbo da kuma Yoruba Wannan aikin na kyauta na gudanane cikin harsunan Hausa da Igbo da kuma Yoruba



Latsa alamar lasifika a hoton da ke sama domin sauraren rahoton Salihu Adamu Usman:

Wata gamayyar kungiyar kwararrun likitoci da ke lura da lafiyar kwakwalwa a Najeriya ta samar da wani layi na kyauta domin taimaka wa masu fama da matsananciyar damuwa da kuma larurar kwakwalwa sakamakon matsalar tsaro dake addabar kasar.

Satar mutane da fashin daji da kuma hare-haren Boko Haram na daga cikin matsalololi da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.

Sannan ba kasafai ake samun cibiyoyin bayar da shawarwari kan lafiyar kwakwalwa cikin harsunan da akafi amfani da su a kasar ba.

Amma wannan aikin na kyauta na gudanane cikin harsunan Hausa da Igbo da kuma Yoruba sannan likitocin na amfani da tarurruka da kuma lika fostoci wajen karfafawa 'yan Najeriya gwiwa su nemi taimako.