BBC Hausa of Sunday, 14 March 2021

Source: BBC

Litinin ce 1 ga watan Sha'aban a Najeriya da Nijar

Hakan na nufin yau Lahadi 14 ga Maris ta zama 30 ga watan Rajab Hakan na nufin yau Lahadi 14 ga Maris ta zama 30 ga watan Rajab

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Sa'ad Abubakar III, ta ce ranar Litinin 15 ga watan Maris ita ce 1 ga watan Sha'aban na Hijira 1442.

Matakin ya biyo gaza ganin jinjirin watan Sha'aban ranar Asabar a faɗin ƙasar, a cewar fadar.

Hakan na nufin yau Lahadi 14 ga Maris ta zama 30 ga watan Rajab.

Kazalika, Litinin ɗin ce 1 ga Sha'aban a ƙasashen Nijar da Saudiyya da Iran da Indonesia da Malaysia da Daular Larabawa (United Arab Emirates) da Oman da Jordan da Falasɗin da Syria da Sudan da Libya.

Sai dai a ƙasashen Masar da Turkiyya da Iraƙi da Tunisiya, yau Lahadi ce 1 ga watan na Sha'aban.

Sha'aban ne wata na takwas a jerin watannin kalandar Musulunci, wanda daga shi sai na Azumin Ramadana mai alfarma.

Bisa ƙa'idar kalandar ta Musulunci, idan aka kasa ganin jinjirin sabon wata a daren 29, akan cika watan ya zama kwana 30 sannan washe gari ta zama 1 ga sabon wata.