BBC Hausa of Tuesday, 20 April 2021

Source: BBC

Liverpool ta leko ta koma a gidan Leeds

Liverpool ta je gidan Leeds United ta tashi 1-1 a wasan mako na 32 Liverpool ta je gidan Leeds United ta tashi 1-1 a wasan mako na 32

Liverpool ta je gidan Leeds United ta tashi 1-1 a wasan mako na 32 a gasar Premier League da suka fafata ranar Litinin.

Tun a minti na 31 da fara wasa Liverpool ta ci kwallo ta hannun Sadio Mane.

Saura minti uku a tashi daga karawar Leeds ta farke ta hannun tsohon dan wasan Sociedad, Diego Llorente.

Da wannan sakamakon Liverpool tana ta shida a kan teburi da maki 53, bayan karawa 32 a fafatawar bana.

Da Liverpool ta hada maki uku a gidan Leeds da ta koma gurbi na hudu kenan a teburi wuri na karshe da za ta iya zuwa Champions League a badi kenan.

Liverpool mai rike da kofi ta yi ban kwana da gasar zakarun Turai ta bana, bayan da Real Madrid ta yi nasara a kanta gida da waje da cin kwallo 3-1.

Yanzu dai Liverpool da alama za ta karkare kakar bana ba tare da cin kofi ba kenan, abin da ke gabanta shi ne kai wa Champions League a badi idan hakan bai yi wu ba ta je Europa League.

Kungiyar ta Anfield wadda ta ci Premier League a bara a karon farko tun bayan shekara 30, ta ci karo da koma bayan da cutar korona ta haddasa da raunin da 'yan wasanta suka dunga jinya.