BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Liverpool za ta dauki mai tsaron bayan RB Leipzig Konate

Mai tsaron bayan RB Leipzig, Ibrahima Konate Mai tsaron bayan RB Leipzig, Ibrahima Konate

Liverpool na zawarcin mai tsaron bayan RB Leipzig, Ibrahima Konate, bayan da ba za ta mallaki Ozan Kabak ba.

Konate mai shekara 22, yana cikin tawagar Faransa ta matasa 'yan kasa da shekara 21 da za su fara gasar Turai ranar 31 ga watan Mayu.

Rahotanni na cewar mai tsaron bayan yana da kunshin kwantiragin fam miliyan 34 ga duk kungiyar dake son daukarsa, idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba.

Liverpool tana da damar kin mallakar Kabak wanda ke buga mata wasan aro daga Schalke, inda ta sanar da dan wasan hakan, shi kuma ya fara tattaunawa da wasu kungiyoyin.

Cikin yarjejeniyar da Liverpool ta shiga wajen dauko Kabak zuwa Anfield a Janairu har da batun mallakar dan kwallon kan fam miliyan 18 idan ya taka rawar gani a kungiyar.

Kabak ya buga wa Liverpool wasa 13 daga baya aka ajiye shi, tun bayan 1-1 da kungiyar ta tashi da Newcastle United ranar 24 ga watan Afirilu.

Konate ya yi wa RB Leipzig wasa 21 a kakar bana, bayan da kungiyar ta karkare kakar Bundesliga a mataki na biyu, za ta wakilci Jamus a Champions League a badi.

Ranar Lahadi Liverpool ta samu gurbin wakiltar Ingila a Champions League a badi, bayan da ta doke Crystal Palace a gasar Premier League ta yi ta uku a teburi.