BBC Hausa of Thursday, 22 April 2021

Source: BBC

Mafi yawan wayoyin hannu a Najeriya na ƙunshe da manhajoji masu hatsari - Bincike

Bincike na nuna wasu wayoyin Android a Najeriya na ƙunshe da miyagun manhajoji na mas Bincike na nuna wasu wayoyin Android a Najeriya na ƙunshe da miyagun manhajoji na mas

Sakamakon wani bincike a Najeriya ya nuna cewa kowace wayar salula guda ɗaya cikin tara masu aiki da tsarin Android, an yi imanin tana ƙunshe da wasu miyagun manhajoji na masu kutse.

Wannan shi ne sakamakon binciken da wani kamfanin fasahar wayoyin salula, mai suna Upstream ya gudanar bayan ya yi nazari kan wasu mu'amaloli har guda 415,000.

Wannan rahoton ya biyo bayan wani nazari na wata uku da aka yi ne. Kuma nasabarsa shi ne a gano zurfin zambar da aka yi a cikin kasar yayin annobar cutar korona, musamman tsakanin watan Nuwamban 2020 da Janairun 2021.

Irin ayyukan wannan mugunyar manhajar na iya kasancewa masu sauki kamar sauya tsarin wayar hannu, amma wasu kuwa na iya kasancewa masu hatsari, inda suke satar kalaman sirri wato passwords da bayanan mai wayar da ya adana a cikinta.

Binciken ya bayyana kimanin manhaja 576 da ke cikin kasar. Upsrtream sun gudanar da binciken ne tare da reshensu mai binciken ƙwaƙwaf kan batutuwan tsaro na intanet mai suna Secure D.

Sun ce yawancin manhajojin na nan a rumbun Play Store na wayoyin hannu masu amfani da tsarin Android.

Rahoton da suka fitar ya lissafta manhajoji biyar da ke ƙunshe da abubuwa da ke damunsu, kamar XOS Launcher, da HiOS Launcher, da Phoenix Browser, da AHA Games da Cobo Launcher Easily DIY Theme.

A cikin yawancin wayoyin Android da ake sayarwa a Najeriya, za a taras da wadannan manhajojin an sanya su.

A misali, wata mahaja mai suna com.android.fmradio, wadda a fuska tana kamo tashohin rediyo samfurin FM ne, an gano cewa da ita aka fi satar bayanai daga wayoyin hannu wanda yawansa ya kai kashi 99.8 cikin 100.

Upstream ya ce kashi 2.6 na dukkan wayoyin hannu ne ke dauke da irin wadannan manhajojin masu hatsari. Ya kuma ce masu samar da manhajojin sun fi kai hare-hare kan wasu kasashen.

Rahoton ya kara da cewa hatsarin fadawa cikin wadanda ake damfara ko sacewa bayanan sirri daga wayoyinsu na hannu ya karu ne saboda kamfanoni da mutane sun rungumi hanyoyin sadarwa na intanet saboda annobar korona ta mamaye duniya.

Shugaban kamfanin Upstream Dimitris Maniatis ya ce mutanen da ba su gama ƙwarewa da tsarin wayoyin hannu ba na iya faɗa wa cikin tarkon da masu samar da waɗannan manhajojin ke kafawa.