BBC Hausa of Thursday, 22 April 2021

Source: BBC

Magoya baya sun jefi 'yan wasan Schalke da kwai

Magoya bayan Schalke 04 sun jefi 'yan wasa da jami'an kungiyar da kwai, bayan da ta fadi daga Bundesliga a karon farko a shekara 33.

Ranar Talata kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Armenia Bielefeld da ci 1-0 a gasar Bundesliga, kuma karawa ta 21 da ta sha kashi a wasannin bana kenan.

Wani dan sandan Gelsenkirchen ya ce tuni magoya baya suka kunna abubuwan tartsatsi da mai futar da hayaki, bayan da kungiyoyin suka tashi daga Bundesliga.

Ranar Laraba 'yan wasa da jami'an Schalke suka je filin wasansu, inda suka tarar da magoya baya sama da 600 na jiran su.

Motar kungiyar na isa magoya baya suka fara zanga-zanga, suka kuma jefi yan wasa da kwai daga fitowarsu daga mota in ji jami'an tsaro.

Da take mayar da martani, Schalke ta ce ''wasu mutane sun keta doka, kuma ba za ta amince da hakan ba.''

Schalke wadda ta yi ta biyu a gasar Bundesliga a 2018 tana daga cikin kungiyoyin da ke da magoya baya da yawa a Jamus, masu bibiyar kungiyar sau da kafa su 60,000 kan shiga kallon wasanninta.