Allah Ya yi wa Hajiya Maryam Ado Bayero matar tsohon sarkin Kano marigayi Ado Bayero rasuwa.
Mai Babban Daki mahaifiya ce ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Majiyoyin masarautar Kano da suka tabbatar wa BBC da labarin rasuwarta, sun ce ta rasu ne a ranar Asabar a ƙasar Masar.
Majiyoyin sun ce ta rasu ne misalin ƙarfe tara na safiyar Asabar. Kuma zuwa gobe ake sa ran yin jana'izarta bayan iso da gawarta zuwa Najeriya daga Masar.
Sanarwar da Masarautar Kano ta fitar ta ce Hajiya Maryam Ado Bayero ta rasu tana da shekara 80 a duniya bayan gajeruwar rashin lafiya.
Hajiya Maryam Bayero Yar sarkin Ilorin ce kuma matar sarki kuma mahaifiyar sarakuna.
Ana kiranta Mai Babban Ɗaki ne saboda kasancewarta uwar Sarakuna.