BBC Hausa of Wednesday, 21 April 2021

Source: BBC

Mahamat Idriss Déby Itno: Abin da ba ku sani ba kan ɗan Idriss Deby, sabon shugaban Chadi

Mahamat tare da uban sa marigayi Idris Deby Itno Mahamat tare da uban sa marigayi Idris Deby Itno

A zahiri, abin da muka sani game da wannan janar din na soja, wanda bai kai shekara 40 ba, ba shi da yawa.

An haifi Janar Mahamat Idriss Déby a 1983 inda ya zama ɗaya daga cikin 'ya'yan marigayi Idriss Deby. Ana masa laƙabi da Mahamat Kaka, saboda a hannun kakarsa ya taso. Kaka na nufin kaka a larabcin Chadi.

A lokacin da mahaifinsa ya mutu, shi ne shugaban dakarun da ke tsaron shugaban kasa, kamar yadda wakilin BBC a Chadi ya bayyana. Wanda ya kara da cewa ya taka rawa a fafatawa da dama da sojoji suka ringa yi a tsawon rayuwarsa ta aiki.

A 2009, Mahamat Idriss Deby ya halarci yakin da Am Dam, wanda aka fafata da wani dan uwansa Timan Erdimi, da ke zama ɗan ɗan uwan tsohon shugaban ƙasar, a gabashin Chadi.

To amma duk da haka, dole ne a bayyana cewa ba fitacce ba ne a lokacin da mahaifinsa ke shugaban ƙasa. Sai dai ya ringa kula da samar da tsaro ga shugaban ƙasa, kuma yana da matukar fada a ji wajen kula da kayan yaƙi na sojojin ƙasar.

Duk da cewa ba shi da wata ƙwarewa wajen tafi da gwamanti, a yanzu Mahamat Deby Itno shi ne zai jagoranci gwamantin riƙon ƙwarya har tsawom wata 18.

A cewa mai magana da yawun rundunar sojan ƙasar, Colonel Azem Bermandoa Agouna, babban aikin majalisar rikon kwaryar da Mahamat yake jagoranta shi ne kare martabar ƙasar da tabbatar da tsaro a cikin gida "a wannan lokaci da ake yaki da 'yan ta'adda kuma dakarun shedan".

Kawu yanzu ba a sani ba ko sabon shugaban gwamnatin ta soja na da wani buri na siyasa.