BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

Man City ta kai wasan karshe a Champions League a karon farko

Kocin Manchester City Pep Guardiola Kocin Manchester City Pep Guardiola

Manchester City ta kai wasan karshe a Champions League, bayan da ta doke Paris St Germain da ci 2-0 a wasan daf da karshe karo na biyu da suka buga a Etihad ranar Talata.

City ta ci kwallayen ne ta hannun Riyad Mahrez, wanda ya zura na farko a minti 11 da fara wasa, sannan ya ci na biyu saura minti 27 a tashi daga fafatawar.

A wasan farko da suka kara a Faransa a makon jiya ranar Laraba, City ce ta yi nasara da ci 2-1 ta kuma kai wasan karshe da cin kwallo 4-1 kenan gida da waje.

Da wannan sakamakon City ta yi nasara a kan PSG sau uku kenan da canjaras biyu a karawa biyar da suka yi a gasar Zakaraun Turai.

PSG wadda take ta biyu a Ligue 1 a teburin bana ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Angel Di Maria jan kati.

Kwazon da Pep Guardiola ya yi a Manchester City a Champions League:

2016-17Zagayen kungiyoyi 16 Manchester City 6-6 Monaco (Monaco ce ta kai zagayen gaba)

2017-18Quarter-final Manchester City 1-5 Liverpool (Liverpool ce ta yi nasara)

2018-19Quarter-final Manchester City 4-4 Tottenham (Tottenham ce ta yi nasara)

2019-20Daf da karshe Manchester City 1-3 Lyon (Lyon ce ta yi nasara)

Mbappe dan kwallon Faransa wanda ya ci kwallo 37 a wasa 43 a dukkan fafatawa a bana, har da guda goma a Champions League, bai buga wasan na Ingila ba.

A bara ne Paris St Germain ta kai wasan karshe a Champions League, inda Bayern ta doke ta da ci 1-0 ta kuma lashe kofin Zakarun Turai na shida jumulla.

Pep Guardiola wanda ya ci Champions League biyu a Barcelona, bai sake yin wannan bajintar ba a Bayern Munich da Manchester City, wadda ya koma a 2017.

Manchester City wadda ta lashe Caraboa Cup na bana kuma na hudu a jere na takwas jumulla, tana ta daya a kan teburin Premier League.