BBC Hausa of Monday, 15 March 2021

Source: BBC

Man United ta ci West Ham ba tare da canja dan wasa ba

United ta buga wasan ba tare da yin canji ba United ta buga wasan ba tare da yin canji ba

Manchester United ta yi nasarar a kan West Ham United da ci 1-0 a wasan mako 29 a Premier League da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi.

West Ham ce ta ci gida ta hannun Craig Dawson da hakan ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata.

United ta buga wasan ba tare da yin canji ba, kuma a karon farko tun fafatawar da ta yi da Liverpool a gasar Premier League cikin watan Fabrairun 2012.

Da wannan sakamakon United ta ci gaba da zama ta biyu a teburi da maki 57 da tazarar maki daya tsakaninta da Leicester City wadda take ta uku.

Wannan ne wasa na 14 da David Moyes ya je Old Trafford ba tare da ya yi nasara ba, illa dai ya yi canjaras hudu aka doke shi fafatawa 10.

Kocin da ya ziyarci United wasanni da yawa ba tare da yin nasara ba, shi ne Harry Rednapp da ya je sau 15 a tarihi a kungiyoyi da dama.

Ita kanta West Ham ta kasa cin United a karawa 12 da ta je Old Trafford a Premier League tun 1-0 da ta ci a 2006/07, ta yi canjaras uku da shan kashi karo tara.

Da wannan sakamakon West Ham wadda ke fatan samun gurbin Champions League a bana tana ta biyar da maki 48 da tazarar maki uku tsakaninta da Chelsea ta hudun teburi.