BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Manjo Janar Farouk Yahaya: Buhari ya naɗa sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya

Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya.

Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis.

Naɗin na zuwa ne kwana shida bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru mai jagorantar rundunar.

Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, da kuma wasu mutum 11 cikin har da janar-janar uku.