Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya.
Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis.
Naɗin na zuwa ne kwana shida bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru mai jagorantar rundunar.
Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, da kuma wasu mutum 11 cikin har da janar-janar uku.
Wane ne Manjo Janar Farouk Yahaya?
An haifi Manjo Janar Farouk Yahaya a garin Sifawa na karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya a shekarar 1966.
Ya shiga aikin soja a 1985 a matsayin dan aji na 37 inda ya kammala karatun soji a ranar 22 ga watan Satumba na 1990.
Ya samu karin girma a rundunar soji kamar haka:
Laftana - ranar 27 ga Satumba 1990
Kyaftin - ranar 27 ga watan Satumba 1994
Manjo - ranar 27 ga watan Satumba 1998.
Laftanar Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2003.
Kanar - ranar 27 ga watan Satumba 2008
Birgediya Janar - ranar 27 ga watan Satumba 2013
Manjo Janar - ranar 27 ga watan Satumba 2017.
Sabon babban hafsan sojin kasan na Najeriya ya yi karatun digirinsa na farko a fannin Tarihi sannan ya yi digiri na biyu wato Masters a kan harkokin siyasar kasashen duniya da difilomasiyya.
Ya rike mukamai daban-daban ciki har da mataimakin sakataren rundunar soji da kuma sakataren na rundunar soji a hedikwatar sojin kasa.
Mukamin da ya rike na karshe kafin naɗin nasa shi na jagorantar yaƙi da Boko Haram karkashin rundunar Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya.
Ya taɓa riƙe muƙamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko wato Geeneral Officer Commanding (GOC) 1 Division.
Kafin nadinsa a mukamin General Officer Commanding 1 Division, Manjo Janar Yahaya ya jagoranci runduna ta 4 da ke hedikwatar rundunar sojin Najeriya.
Kazalika ya rike mukamin Kwamandan rundunar Lafiya Dole da ke Maiduguri, a jihar Borno.
A shekarar 2019, Manjo Janar Farouk Yahaya ya jagoranci rundunar Operation CLEAN SWEEP wadda ta fatattaki 'yan bindigar da ke dajin Kuduru a Birnin Gwari na jihar Kaduna.