Manuel Neuer zai zama mai tsaron raga na farko da zai yi wa tawagar kwallon kafar Jamus wasa na 100 ranar Litinin.
Ranar Litinin Jamus za ta buga wasan sada zumunta da Latvia, domin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Turai da za a fara a watan gobe, kuma gasa ta shida da zai halarta.
Neuer, mai shekara 35, zai yi murnar wannan bajintar a gaban 'yan kallo 1,000 a filin wasa da ke Dusseldorf a Jamus.
Mai tsaron ragar Bayern Munich ya fara yi wa tawagar Jamus tamaula cikin shekarar 2009 a karawar da kasar ta doke Hadaddiyar Daulal Larabawa da ci 7-2.
Neuer shi ne mai tsaron raga na farko da zai buga wa Jamus karawa ta 100, kuma na 16 jumulla a kasar da suka yi wannan kwazon, inda Lothar Matthaeus ke kan gaba mai fafatawa 150.
Tun cikin farkon shekarar nan ya kamata Neuer ya yi wa Jamus karawa ta 100 jumulla, amma rauni da ya dunga jinya ya sa ya ci karo da cikas.
Jamus ta yi fitattun masu tsaron raga a baya da suka hada da Sepp Maier da Oliver Kahn da kuma Toni Schumacher, amma ba wanda ya yi wa kasar fafatawa 100 a tamaula a tarihi.
Da zarar an kammala gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana, Joachim Loew zai ajiye aikin jan ragama, inda Hansi Flick zai ci gaba daga inda aka tsaya.
Ana kuma ganin cewar tsohon kocin Bayern Munich, Flick zai ci gaba da amfani da Neuer a tsakanin turakan Jamus a fannin taka leda.