Fitacciyar marubuciyar nan, 'yar gwagwarmaya kuma likita ta kasar Masar Nawal El Saadawi, wadda ake bayyanata a matsayin ta daya a duniya daga kasashen Larabawa wajen fafutukar tabbatar da 'yancin mata ta rasu a birnin Alkahira.
Dakta Nawal wadda ta kasance tana jinya tsawon wani lokaci, ta rasu tana da shekara tamanin da tara a babban birnin kasar ta Masar.
Nawal El Saadawi ta yi fice tare zama jigo wajen gwagwarmaya da fitowa da batutuwan da suka jibanci 'yancin siyasa da tabbatar da hakkin mata a duk wani fanni na rayuwarsu a Masar.
Ta rubuta littattafai sama da hamsin, da suka hada da fitaccen littafinta da aka fassara a harsuna da dama, mai suna 'Woman at Point Zero'.
An dai haramta da dama daga cikin littattafai da rubuce-rubucen da ta yi a kasar ta Masar, tsawon gomman shekaru.
Kuma a shekara ta 1981 an daure Nawal, a lokacin mulkin Shugaba Anwar Sadat, saboda irin ra'ayinta wanda ba ta saurarawa wajen bayyanawa.
Haka kuma ta yi zaman gudun hijira na wasu shekaru a Amurka kafin daga baya ta koma Masar din a cikin shekarun 1990.
Farfesa Miriam Cooke, kwararriya a kan al'adun Larabawa a Jami'ar Duke da ke Amurka, wadda kawa ce ta kut da kut ga Dakta Nawal, a hirarata da BBC ta ce abiyar tata, mace ce mai jajircewa a kan duk wani abu da ta yi amanna da shi.
Ta ce, "ko alama ba ta yadda za a yi ta bayar da kai bori ya hau ga duk wani abu da ke da alamun rashin adalci. Saboda haka 'yar gwagwarmaya ce ta hakika.
"A duk lokacin da za mu hadu, za ka ga ko da yaushe tana da wani aiki babba da ta sa a gaba, kuma wannan aiki a ko da yaushe za ka ga abu ne na duniya, a kan abun da za mu yi tare, kuma da haka za mu kai ga samun gagarumar hadaka ta gwagwarmaya kuma mu kai ga haifar da sauyi a duniya....."
Babban abin da Dakta Nawal ta ba wa fifiko dai shi ne yaki da al'adar yi wa mata kaciya, abin da aka yi mata tana karama. Kuma wannan gwagwarmaya tata ce ta kai ga Masar ta haramta al'adar a shekara ta 2008.
A shekarar da ta wuce, 2020 mujallar Time Magazine ta sanya ta a matsayin daya daga cikin gwarazan matanta dari daya na shekara.